Babbar Magana: 'Yan Bindiga Sun Sace Babban Alkali a Najeriya

Babbar Magana: 'Yan Bindiga Sun Sace Babban Alkali a Najeriya

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza
  • Hatsabiban 'yan bindigan sun yi awon gaba da shi daga gidansa da ke kan titin Zogirma a ƙaramar hukumar Bunza
  • Rundunar ’yan sanda ta tura jami’an leƙen asiri da na musamman domin ceto alkalin wanda ya fada komar 'yan bindiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Bunza, Kebbi – Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da Alƙalin Babbar Kotun Jihar Kebbi, Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza, a gidansa da ke kan titin Zogirma a ƙaramar hukumar Bunza.

An tattaro cewa lamarin ya faru da tsakar daren Asabar zuwa Lahadi, da misalin ƙarfe 12:00 na dare, jim kaɗan bayan alƙalin ya dawo daga wata tafiya zuwa Sokoto.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace babban dan siyasa, matarsa da 'ya'yansa a Zamfara

'Yan bindiga sun sace alkali a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun sace alkali

Wata majiya da ta zanta da wakilin jaridar Daily Trust ta ce ’yan bindigan sun kutsa cikin gidan alƙalin tare da yin awon gaba da shi.

“Ya dawo daga Sokoto ne, sai ’yan bindigar suka mamaye gidansa suka tafi da shi,” in ji majiyar.

Ta ƙara da cewa babu wanda ya ji rauni a gidan, duk da cewa maharan sun riƙa harbe-harbe lokaci-lokaci kafin su tafi da alƙalin.

“Nan take bayan faruwar lamarin, muka kai rahoto ga hukumomin da abin ya shafa, ciki har da shugabannin Babbar Kotun,” in ji ta.

Rundunar ’yan sanda ta fara neman alƙalin

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, SP Bashir Usman, ya tabbatar da sace alƙalin.

“Zan iya tabbatar da cewa an yi garkuwa da Mai Shari’a Faruku Hassan Bunza daga gidansa da ke Bunza da misalin tsakar dare.” In ji shi

SP Bashir ya ce bayan samun rahoton sace shi, kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Umar Muhammad Hadejia, ya tura jami’an musamman da na leƙen asiri domin tabbatar da an ceto shi cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Ba adalci: Kanawa sun yi martani da Gwamna ya raba filaye, N100m ga yan dangwale

“Yayin da muke magana, jami’anmu na binciken wuraren da aka gano, ciki har da yankunan dazuzzuka, domin tabbatar da an ceto alƙalin da ransa kuma ba tare da an cutar da shi ba,” in ji jami’in.

Babbar Kotu ta bayyana damuwa

Wani babban jami’i a Babbar Kotun Jihar Kebbi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin babban abin takaici ga bangaren shari’a.

“Ba a ba ni izinin yin magana a hukumance ba, amma wannan lokaci ne mai raɗaɗi a gare mu. Jin cewa an yi garkuwa da ɗaya daga cikin alƙalanmu a gidansa abin damuwa ne ƙwarai,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa mahukuntan Babbar Kotun sun riga sun gana da shugabannin hukumomin tsaro a jihar domin tsara yadda za a tabbatar da sakin alƙalin cikin gaggawa.

'Yan bindiga sun sace alkalin babbar kotun Kebbi
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi Hoto: Nasir Idris Kauran Gwandu
Source: Facebook

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin sace alƙalin.

'Yan bindiga sun yi barna a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Yan bindiga dauke da makamai sun kashe manoma a wani hari sa suka kai a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun kashe akalla manoma 23 a kauyen Sauna/Ruwan Gora da ke karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com