Gwamna Abba Zai Kafa Kamfanin Jirgin Sama na Kano, an Sanya Lokacin Fara Aikinsa
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da shirin kafa kamfanin jirgin sama mallakar gwamnatin jihar Kano
- Kamfanin da za a kafa zai samar da guraben aiki ga ‘yan asalin Kano da suka kammala horon tukin jirgin sama
- Kungiyar matukan jiragen sama ta jihar Kano ta yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan tallafin da gwamnatinsa take ba su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da shirin gwamnatinsa na kafa kamfanin jirgin sama mallakar jihar domin samar da guraben aiki ga ‘yan asalin Kano da suka kammala horon tukin jirgin sama.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron majalisar zartarwar jihar Kano karo na 40 da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Kano.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Alhamis, 23 ga watan Yulin 2026 a shafinsa na Facebook.
A wajen taron, Gwamna Abba ya karbi lambobin yabo da dama, ciki har da karramawa daga Kungiyar Matuka Jirgin Sama ta Jihar Kano saboda goyon bayan da ya ba mambobinta wajen kammala horon harkar jiragen sama.
Yaushe kamfanin zai fara aiki?
A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, ana sa ran kamfanin jirgin saman zai fara aiki cikin shekara guda mai zuwa.
Gwamna Abba ya ce kamfanin zai zama wata hanya ta daukar ‘yan asalin Kano da suka kammala horon zama matuka jirgin sama, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta samar da tallafin da ake bukata domin ganin an fara aikin cikin nasara.
“Da yardar Allah, ana sa ran kamfanin jirgin saman Kano da ake shirin kafawa zai fara aiki cikin shekara guda mai zuwa,” in ji gwamnan.
Gwamna Abba ya yabawa matuka jirgi
Ya kuma bayyana gamsuwarsa da yadda matukan jirgin da gwamnatin Kano ta dauki nauyin horarwa a Jordan suka gudanar da ayyukansu.
An fara shirin horar da matukan ne a karkashin wata gwamnati da ta gabata, inda ya bayyana nasarorin da suka samu a matsayin abin karfafa gwiwa.
Gwamnan ya sake tabbatar da kudirin gwamnatinsa na tallafa wa bangaren zirga-zirgar jiragen sama tare da tabbatar da cewa an samar wa matukan jirgin da suka samu horo damar bayar da gudummawarsu wajen ci gaban jihar.

Source: Facebook
Kungiyar matuka ta yaba
Tun da farko, shugaban Kungiyar Matuka Jirgin Sama ta Jihar Kano, Naziru Ibrahim, ya yabawa gwamnan saboda taimakawa wajen sabunta lasisin tukin jirgin sama na mambobin kungiyar, yana mai bayyana matakin a matsayin babban ci gaba ga sana’ar matukan jirgin.
Ya roki gwamnan da ya kara taimaka wa mambobin kungiyar wajen samun takardun shaidar karshe, wadanda za su ba su damar gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci a cikin Najeriya da kuma kasashen duniya.
Matakin magance shaye-shaye da daba a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya ƙaddamar da wani kwamitin haɗin gwiwa na hukumomi daban-daban domin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.
Gwamnan ya kuma sanya hannu kan wani umarnin zartarwa da zai ƙarfafa matakan yaƙi da daba da sauran ayyukan laifi a jihar Kano.
Asali: Legit.ng

