Jihar Legas
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 20 ga watan Dasumba, zai kaddamar da wani katafaren aiki da aka kamalla ginin sa a tashar jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe International Airport da ke birnin Abuja.
Majiyar Legit.com ta ruwaito wannan rikici ya faru ne a wata unguwa dake cikij garin Legas Badia Ijora, inda matasan kungiyar matsafa ta Aye da na Eiye suka far ma junansu ba kakkautawa, a dalilin haka ne mutane bakwai suka mutu.
Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya, NPA, ta bayyana cewa akalla manyan jiragen ruwa da aka fi sani da suna jirgin dankaro guda talatin da shida (36) ne suka nufo Najeriya makare da tataccen man fetir da kayayyakin ma
Majiyar Legit.com ta ruwaito hukumar NPA tace tana sa ran jiragen zasu fara isowa Najeriya ne daga ranar Litinin 26 ga watan Nuwamba zuwa 30 ga watan Nuwamba, muma suna dauke ne da tataccen man fetir da kayan abinci.
Za ku ji yadda wasu manyan APC su ka nemi su ceci Ambode amma aka gaza a Legas. Ana ji ana gani Gwamna mai-ci Akinwunmi Ambode ya sha kasa Babajide Sanwo-Olu a hannun wanda Asiwaju Bola Tinubu ya tsaida a Jam’iyyar APC.
Sakamakon zaluntarsu da suka ce tana musu ne suka yanke shawarar yin garkuwa da ita, shirin da ya daukesu kwanaki goma suna tsara yadda zasu yi awon gaba da matar, tare da riketa har sai an biyasu makudan kudaden fansa.
Daga nan ne Ibeh ya harzuka, inda ya kai ma Moreni naushi, shi kuma ganin haka ya sauka kasa, inda ya dauko kwalba, ya fasata ya nufi Ibeh da gudu, isarsa kansa keda wuya ya caka masa a wuya, kafin a ankara jini ya fara kwarara.
Daga cikin jihohin Najeriya masu muhimmanci akwai jahar Legas, jahar da tafi kowace jaha arziki a Najeriya, kuma jaha ta biyu wajen yawan jama’a a Najeriya, bayan jahar Kano, kaar yadda alkalummar hukumar kidaya suka nuna.
Majiyar LEGIT.com ta ruwaito lamarin ya faru ne da safiyar Alhamus 25 ga watan Oktoba, sai dai babu tabbacin abinda ya sabbaba wannan hatsari mai muni zuwa lokacin da muka tattara rahoton, amma shanu da dama sun samu munanan rauni
Jihar Legas
Samu kari