Yahoo-Yahoo: Kotu ta yanke wa uwa da 'dan cikinta hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari

Yahoo-Yahoo: Kotu ta yanke wa uwa da 'dan cikinta hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari

A ranar Laraba ne hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki ta sanar da cewa wata kotun tarayya ta yanke wa wata uwa sa dan cikinta hukunci bayan samunsu da laifin damfara.

Jastis Chukwujekwu Aneke, alkalin kotu, wacce ke zamanta a Ikoyi, jihar Legas, ya yanke wa matar, Alaba Kareem Adeyeri, da dan cikinta, Damilola Ahmed Adeyeri, hukuncin daurin as goma sha biyu a gidan yari bayan hukumar EFCC ta gurfanar dasu bisa tuhuma guda hudu.

Ana tuhumar uwar da danta da laifin hada baki tare da samun kudi $82,570 ta hanyar damfara ta yanar gizo, wacce aka fi sani da 'Yahoo-Yahoo'.

A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa ranar Talata, kun ji cewa Tsohon shugaban kwamitin wucin gadi da majalisar wakilai ta kafa domin binciken biyan tallafin man fetur a 2012, Farouk Lawan, ya sanar da babbar kotun Abuja cewa dan uwan shaidarsa na farko da zai gabatar ya mutu ranar Lahadi bayan kamuwa da zazzabin Lassa a Kano.

Tsohon dan majalisar ya bayyana hakan a gaban kotun yayin zamanta na ranar Talata.

Lawan, ya fadi hakan ne a matsayin hujjarsa ta kin fara kare kansa a tuhumar da aka fara yi masa tun shekarar 2012.

Yahoo-Yahoo: Kotu ta yanke wa uwa da 'dan cikinta hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari
Uwa da 'dan cikinta da aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 12 a gidan yari
Asali: Twitter

Ana tuhumar Lawan da kabar cin hancin dalar Amurka $500,000 domin cire sunan kamfanin man fetur da iskar Gas mallakar hamshakin dan kasuwa, Mista Femi Otedola.

A ranar 17 ga watan Oktoba na shekarar 2019 ne alkaliyar kotun dake sauraron karar da aka shigar da Lawan tayi watsi da uzurin Lawan na cewa bashi da wani laifi balle ya kare kansa, ya bayyana hakan ne bayan bangaren masu kara sun gabatar da shaidu biyar.

DUBA WANNAN: Bauchi: Saurayi mai kishi ya caka wa budurwarsa wuka saboda ta amsa kiran wani a gabansa

Jastis Angela ta umarci Lawan ya fara shirin kare kansa a tuhumar da ake yi masa, saboda an gabatar da shaidu masu karfi a kan tuhumar da ake yi masa. Kotun ta umarce shi ya fara kare kansa daga ranar 11 ga watan Nuwamba, 2019, amma saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba sai kotun ta daga zamanta zuwa ranar Talata, 28 ga watan Janairu, 2020.

Amma, bayan kotun ta zauna a ranar Talata, sai lauyan dake Lawan, Mista Benson Igbanoi, ya sanar da cewa ba zasu iya fara kare kansu ba saboda shaidarsu guda daya "jalli jal" ya rasa dan uwansa, wanda mutu ranar Lahadi a Kano bayan ya kamu da zazzabin Lassa, a saboda haka bai samu damar halartar zaman kotun ba.

Lauyan masu kara ya tabbatar wa da kotun cewa lauyan wanda ake kara ya aika masa da takarda ranar Litinin domin sanar sa shi batun mutuwar dan uwan shaidan.

Alkaliyar kotun ta daga sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel