Tirkashi: Wani mutumi ya siyawa karuwarshi dankareren gida, bayan matarshi ta neme ta da fada

Tirkashi: Wani mutumi ya siyawa karuwarshi dankareren gida, bayan matarshi ta neme ta da fada

- Jaruma Damilola Adegbite ta wallafa wani labarin da ya jawo hankalin mutane

- Matar wani magidanci ce ta tattara kawayenta kuma suka kai hari ga karuwar shi a gidan da take haya

- Daga baya magidancin ya sallami matar shi tare da siya wa karuwar gida a Ikoyi da kuma masu tsaron lafiyarta

'Yar wasan kwaikwayon masana'antar Nollywood, Damilola Adegbite ta bada wani labari mai ban mamaki a Instagram.

Wani dan Najeriya ya yanke hukuncin siya wa karuwar shi gida a Ikoyi bayan matar shi ta kwashi kawayenta inda suka je har gidan da take haya don kai mata hari.

Kamar yadda Damilola ta bayyana, mutumin ya kori matar tashi daga gidan shi bayan ya siya wa karuwar tashi gidan.

"Ya kori matar tashi kuma. Da kanka zaka dora wa kanka hawan jini. Idan ka mutu, namiji kuka zai yi na kwanaki kadan kafin ya cigaba da sha'anin shi. Wannan rayuwar mai sauki ce, tashin hankali bashi da dadi ko kadan." Cewar jarumar.

KU KARANTA: Tashin hankali: Kyakkyawar budurwa ta kashe kanta saboda ta rasa masoya a dandalin Instagram

Jaruma Damilola ta wallafa cewa, ta je duba wani gida ne da zata karba haya a Legas. A wajen duba gidan ne ta ga gidan lafiya lau da kuma kaya a ciki. Amma gilasan tagogin ne suka farfashe kamar anyi amfani da duwatsu wajen fasa su.

"Bayan da na tambaya sai agent din ya sanar dani cewa wata karuwa ce ta tashi daga gidan. Tana soyayya ne da wani magidanci amma sai ya siya mata gida a Ikoyi bayan matar shi da kawayenta sun hare ta. A halin yanzu har da masu tsaron lafiyarta take tafiya kuma mijin ya sallami matar shi a kanta."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel