Mai dokar barci: An kama masu gadin bututun mai su 20 da laifin satar man fetir

Mai dokar barci: An kama masu gadin bututun mai su 20 da laifin satar man fetir

Akalla jami’ai guda 20 da hukumar man fetir ta kasa, NNPC, ta dauka aikin kare mata bututun man ta ne suka shiga hannu sakamakon kama su da aka yi da laifin fasa bututun mai tare da haka rijiyoyin man fetir guda 310.

Rahoton Daily Trust ya bayyana daga cikin wadanda aka kama akwai jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, Civil Defence wanda aka turasu domin su yi gadin bututun mai daga Atlas Cove, zuwa tashar man fetir ta Ejigb dake Legas da na Mosimi dake Ogun.

KU KARANTA: An yi asarar haihuwa: Matashi ya kashe mahaifinsa saboda rikici a kan Doya a Ebonyi

Kwamanda Thomas Otuji na rundunar Sojan ruwan Najeriya ya bayyana Sojojinsa ne suka kama masu gadin a lokacin da suke gudanar da atisayen ‘Operation Kunronbe’ a yankin da aka binne bututun man.

Kwamanda Thomas ya ce a yanzu haka barayin su 20 suna can a daure a cikin jirgin Sojan ruwa mai suna BEECROFT dake Apapa inda suke amsa tambayoyi. Ya kara da cewa ana haka rijiyoyin man ne domin antaya man fetir a cikinsu.

Wasu daga cikin rijiyoyin an haka su ne a cikin sansanin masu gadin, wasu kuma a gaban sansanin aka haka su, wanda hakan ya nuna sa hannun masu gadin cikin wannan mummunan aikin na cin amanar kasa, inji kwamandan.

Daga karshe ya ce daga cikin kayayyakin da suka gano akwai karafan zuko mai, da tiyo tiyo da dama wanda suke jonasu a jikin bututun main a NNPC domin su zuko man fetir, haka zalika sun warware sama da wurare 300 a jikin bututun.

A wani labarin kuma, Malam Ibrahim Magu ya bayyana cewa zasu dauki sabin tsauraran matakai a kan barayin dukiyar jama’a, musamman barayin mai a yankin Neja Delta.

Magu ya ce idan suka kammala dabbaka sabbin tsauraran matakan nasu, barayin ba zasu sake samun wani katabus na yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa ba, musamman a cikin sabuwar shekarar 2020.

“Yankin Neja Delta na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin kasa, don haka hukumar EFCC ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar an hukunta dukkanin masu satar mai tare da fasa bututun mai.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng