Jerin jihohi 15 da suka fi cin bashi a Najeriya
- Jimillar bashin da ake bin kasar Najeriya ya kai naira tiriliyan 4.04 wanda yayi dai-dai da dala biliyan 11.17 a watan Satumba na 2019
- Akwai wasu jihohi da ke da tarin bashin wanda hakan ya taka rawar gani wajen hauhawar bashin Najeriya
- Jihohin Legas, Rivers da Delta ne ke kan gaba a cikin jerin jihohin da suka fi kowanne yawan bashi a Najeriya
Jimillar bashin da ake bin Najeriya ya kai naira tiriliyan 4.04 wanda dai-dai yake da dala biliyan 11.17 a watan Satumba na 2019. Jihar Legas ce ke da kashi 10.9 na jimillar bashin.
Jaridar Business Insider ta binciko jihohi 15 a Najeriya da suka fi sauran jihohin yawan bashi a watanni uku na karshen 2019.
Jihar Legas ake bi bashin dala biliyan 1.2 wanda yayi dai-dai da kashi 10.9 na jimillar bashin da ake bin kasar nan baki daya, kamar yadda hukumar kiyasi ta Najeriya ta bayyana.
A cikin jihohin da suka fi ko ina yawan bashi akwai jihohin Legas, Ribas da Delta. Su ne suka bayyana da mafi yawan bashi a cikin jihohi 36 na Najeriya, har da babban birnin tarayya, Abuja.
Jihar Yobe ce ke da mafi karancin bashi a jihohin Najeriya. Jihar ce ke da kashi 0.7 na jimillar bashin da ake bin Najeriya.
KU KARANTA: An yiwa 'yar gidan mai kudin duniya Bill Gates baiko da Musulmi dan Afrika
Ga jerin jihohi 15 na kasar nan masu yawan bashi kamar yadda jaridar Business Insider SSA ta ruwaito.
Jihar Legas na da bashin naira biliyan 441.67, jihar Ribas na da bashin naira biliyan 266.94, jihar Delta na da bashin naira biliyan 230.57 inda jihar Akwa Ibom ke da bashin naira biliyan 237.40.
Jihar Cross River na da bashin naira biliyan 167.97, jihar Imo na da bashin 148.90, jihar Osun na da bashin naira biliyan 141.79 sai kuma jihar Ogun na da bashin naira miliyan 140.99.
Babban birnin tarayya, Abuja na da bashin naira biliyan 137.86, jihar Bayelsa na da bashin naira biliyan 127.24 sai jihar Kogi da ke da bashin naira biliyan 117.34.
Jihar Kano wacce ita ce cibiyar kasuwancin arewa tana da bashin naira biliyan 117.34, jihar Filato na da bashin naira biliyan 108.97, jihar Bauchi na da bashin naira biliyan 105.20 inda jihar Binuwai ke da bashin naira biliyan 98.44.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng