Tonon silili: Mijina fitaccen dan luwadi ne, a Legas suke yin iskancin su - Matar aure

Tonon silili: Mijina fitaccen dan luwadi ne, a Legas suke yin iskancin su - Matar aure

- Lamarin auratayya cike yake da jarabawa mai tarin yawa a wannan zamani

- Wata matar aure ta bayyana cewa ta bankado mijinta dan luwadi ne a shekarar da ta gabata

- Bayan bayyana wa 'yan uwa da abokan arziki, ta shirya tsinke auren a wannan sabuwar shekarar

Al'amarin auratayya a wannan zamani sai dai fatan dace na alkhairi. Kasancewar aure ibada ce, dole akwai kalubale kala-kala da ma'aurata kan fuskanta. Wasu kalubalen kanana ne don ana iya jurewa, wannan shine ake kira da hakurin aure. Wasu kuwa manyan ne kuma banbance-banbance ne da ba a iya shawo kansu.

Wata mata ta koka da irin kaddarar da ta fada mata a gidan aurenta. Ta bankado cewa mijinta na cin amanarta amma ba da wata mace ba. Ta gano cewa maigidan nata dan luwadi ne.

Matar auren ta bayyanawa masanin zamantakewa da soyayya, Joro Olumofin halin da ta tsinci kanta a shekarar da ta gabata.

KU KARANTA: Rikicin Boko Haram: Zulum ya bawa sojoji da 'yan sanda motoci guda 70 na aiki

"Joro, mijina dan luwadi ne kuma na gane hakan a shekarar da ta gabata. Abokin barnar shi yana da mata a Lekki. A wannan shekarar zan kashe aurena. 'Yan uwana mata, zata yuwu mazanku 'yan luwadi ne. Maza da yawa na luwadi a yau, aurenmu mata suke yi don rufa wa kansu asiri." Cewar matar auren.

Kamar yadda tace, bayan tuntubar 'yan uwa da abokan arziki, ta yanke shawarar tsinke aurenta a wannan shekarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel