Abin da Ƴan Najeriya ke Cewa kan Bidiyon Sarkin Daura da Baturiya ke Zarginsa

Abin da Ƴan Najeriya ke Cewa kan Bidiyon Sarkin Daura da Baturiya ke Zarginsa

  • Ana ci gaba da samun martani kan zargin cin zarafin lalata da ake yi wa Sarkin Daura, Umar Faruk Umar a wani faifan bidiyo
  • Wani dan Najeriya da kuma mazauna Kano da Katsina sun bayyana zargin a matsayin abin kunya, inda suka bukaci gudanar da bincike
  • Amnesty International da wasu fitattun mutane sun bukaci a gudanar da bincike kan zargin domin daukar mataki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Daura, Katsina - Zargin cin zarafin lalata da ake yi wa Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya.

Wasu yan Najeriya da mazauna gari da kungiyoyin fararen hula suka bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa.

An yada bidiyon sarkin Daura da wata baturiya
Mai martaba Sarkin Daura, Umar Farouk Bashir Hoto: Masarautar Daura.
Source: Facebook

Abdullateef Abubakar, mawallafin jarida da ke Kano, ya bayyana zargin a matsayin abin kunya ga kasa, yana mai cewa lamarin ya haifar da tambayoyi kan halayen da ake bukata daga sarakunan gargajiya, cewar ThisDay.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da matar da ake zargin Sarkin Daura ya taɓa jikinta

Yadda ake neman bincike kan Sarkin Daura

Abubakar ya bukaci a gudanar da cikakken bincike, yana mai cewa bai kamata a yi wasa da zargin lalata ba ko a boye shi saboda matsayin wanda ake zargi.

Haka kuma, Musa Mudi, wani mazaunin Katsina, ya ce lamarin ya bata sunan masarautar gargajiya, inda ya bukaci hukumomi su gudanar da bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Mudi ya kuma bukaci gwamnatocin tarayya da jihohi su kara daukar matakan dakile cin zarafin mata, tare da tabbatar da cewa wadanda abin ya shafa za su iya kai rahoto ba tare da fuskantar barazana ba.

Yadda zargin ya fara

Rikicin ya samo asali ne bayan wata matafiyar kasashen waje mai suna Mirka, wadda ke amfani da shafin sada zumunta na @beduinqa, ta wallafa wani faifan bidiyo a intanet.

Matar, wadda ta ziyarci Najeriya na tsawon kwanaki 30, ta yi zargin cewa an ci zarafinta ne lokacin da ta kai ziyara fadar Sarkin Daura ranar 14 ga Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya nemi a dakatar da Sarkin Daura kan zargin taba baturiya

Ta yi zargin cewa sarkin ya rike hannunta, ya rungume ta sannan ya sumbaci kumatunta ba tare da izininta ba. Ta kuma ce ya taba jikinta ta hanyar da ba ta amince da ita ba duk da nuna rashin yardarta.

Matar ta bayyana cewa ta dauki bidiyon ne ta amfani da tabaran zamani na Meta, kafin daga bisani ya bazu a kafafen sada zumunta.

An taso sarkin Daura a gaba
Yar yawon bude ido, Mirka Cze da Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk Hoto: Daura Emirate, @beduinqa.
Source: Facebook

Amnesty ta bukaci bincike mai zaman kansa

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International Nigeria ta bukaci gwamnatin Katsina da rundunar 'yan sanda su gudanar da bincike mai zaman kansa da gaskiya kan zargin.

Kungiyar ta jaddada cewa dole ne a tabbatar da bin doka da kuma daukar matakin da ya dace, ba tare da la'akari da matsayin ko tasirin wanda ake zargi ba.

Muhimmancin kare hakkin mata

Lamarin ya kuma sake jawo hankali kan matsalar cin zarafin mata a Najeriya, musamman wahalhalun da wadanda abin ya shafa ke fuskanta wajen neman adalci idan masu fada-a-ji suke cikin wadanda ake zargi.

Masu sharhi sun ce yadda hukumomi za su gudanar da binciken zai taimaka wajen tabbatar da amincewar jama'a da kuma nuna cewa babu wanda yake sama da doka.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya yi kira a tunbuke duk sarkin da aka samu ya yi aikin assha

Sun kuma jaddada bukatar samar da ingantaccen tsarin kare mata, binciken korafe-korafen cin zarafi da kuma hukunta wadanda aka tabbatar sun aikata laifi, cewar Leadership.

An bukaci sauke Sarkin Daura

Mun ba ku labarin cewa Tsohon gwamnan Kaduna, Kanal Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya), ya buƙaci Gwamna Dikko Umar Radda na Katsina ya dakatar da Sarkin Daura.

Dangiwa ya nemi a dakatar da sarkin ne domin gudanar da bincike kan zargin cin zarafin wata mata ’yar ƙasar waje da ake dangantawa da shi.

Ya ce idan bincike ya tabbatar da zargin, ya kamata a sauke sarkin daga kan karagarsa ba tare da ɓata lokaci ba domin kare martabar masarautar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.