Abin mamaki: An ruwan damina na farko a jihar Legas

Abin mamaki: An ruwan damina na farko a jihar Legas

- Mazauna jihar Legas sun shiga tsananin mamaki bayan da aka yi ruwa na farko a watan Janairu na 2020

- A jiya ne wajen karfe biyu na yamma aka yi mamakon ruwan sama wanda ya jawo ambaliyar ruwa a wasu yankunan jihar Legas

- Ruwan da ya dau tsawon mintina 30 ana yi, ya fara ne bayan da gagarumin hadari ya hadu a sararin samaniya

Mazauna jihar Legas sun shiga tsananin mamaki bayan da aka yi ruwan sama na farko a shekarar 2020 a jihar.

Anyi ruwan saman ne a jiya wajen karfe 2 na yamma wanda ya dau mintuna 30, lamarin da ya jawo ambaliyar ruwa mai karfi.

Mazaunan jihar da yawa basu yi tsammanin zuwan ruwan sama a wannan lokacin ba. An ga wasu hadari ne sun taru a sararin samaniya. An fara ruwan saman ne wanda yasa masu tafiya a kasa, 'yan kasuwa da jama'ar da basu da kariya neman mafaka.

A Ikeja, wani bangare na titin Awolowo, Adeniji Jones da Allen Avenue duk ambaliyar ruwan ta mamaye. Mutane da yawa da ruwan saman ya ritsa dasu duk sun jike.

KU KARANTA: Saurayi ya yiwa 'yar bautar kasa fyade ya kuma dauki bidiyonta tsirara

Wani mazaunin yankin mai suna Ola Adegoke, wanda ya kwatanta ruwan da abun mamaki yace ruwan ya taimaka wajen rage tsananin zafin da jama'a ke fuskanta a cikin makonnin da suka gabata.

"Wannan ruwan ya rage mana tsananin kura da muke fama da ita a makonnin da suka gabata."

Har yanzu dai ba a gano cewa ko duk fadin garin ne aka yi wannan ruwan ba, amma wannan yankin bai samu ruwan sama ba kwata-kwata har zuwa watan Disamba na 2019 sai a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel