An Ware Mazabun da za a Yi Zaben Shugaban Kasa na Gwaji a Najeriya

An Ware Mazabun da za a Yi Zaben Shugaban Kasa na Gwaji a Najeriya

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta zaɓi rumfunan zaɓe 17,676 a faɗin Najeriya domin gudanar da gwajin na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS
  • Hukumar ta ce za a gudanar da gwajin ne a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, 2026, daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana
  • Za a yi gwajin ne a rumfunan zaɓe biyu a kowace mazaba inda za a yi shi a mazabu 8,838 da ke faɗin ƙasar, gabanin babban zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen rumfunan zaɓen da za ta yi amfani da su wajen gwajin na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS da loda sakamakon zaɓe ta intanet.

Kara karanta wannan

Yadda za ka gane idan kana cikin wadanda gwamnati za ta turawa tallafin N100,000

Hakan na zuwa ne yayin da hukumar ke shirye-shirye domin tabbatar da cewa ba a samu wata matsala ba a zaben shugaban kasa da ke tafe.

Shugaban hukumar INEC
Shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Hukumar ta sanar da hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X ranar Litinin. Ta kuma bayyana cewa za a gudanar da gwajin a rumfunan zaɓe biyu a kowace mazaba daga cikin 8,838 da ke faɗin Najeriya.

Abin da INEC za ta gwada

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce an shirya gwajin ne domin tabbatar da ingancin na’urar BVAS, duba yadda ake tantance masu zaɓe da kuma gano duk wata matsalar fasaha da ka iya tasowa kafin zaɓen 2027.

Punch ta wallafa cewa INEC ta ce za a gudanar da aikin daga ƙarfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na rana a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, 2026.

Hukumar ta kuma buƙaci masu ruwa da tsaki da sauran jama’a su shiga shafinta domin duba jerin rumfunan zaɓen da aka zaɓa domin gwajin.

INEC ta bukaci mai son ganin jerin mazabun da za a yi zaben gwajin a nan domin tabbatar da ko mazabar shi tana cikin wuraren da gwajin ya shafa.

Kara karanta wannan

Ciyaman a Kano ya ballo ruwa, ya yi barazana ga jama'a kan zaben APC a 2027

Wajen zabe a Najeriya
Masu kada kuri'a yayin zaben cike gurbi a Gombe. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

ADC ta nemi a ɗage ranar gwajin

Sanarwar ta zo ne a lokacin da wasu ’yan siyasa suka nuna damuwa kan ƙarancin lokacin da INEC ta ba jam’iyyun siyasa domin shirin gwajin.

A ranar 18 ga Nuwamba, kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC ya buƙaci INEC ta ɗage aikin, yana mai cewa sanarwar da aka bayar ba ta ba jam’iyyun isasshen lokacin tattara wakilai, horas da su da kuma shirya halartar gwajin ba.

Kwamitin ya bayyana cewa lokacin da aka bayar bai wadatar ba, don haka ya nemi hukumar ta ba jam’iyyun damar yin shiri yadda ya kamata domin su taka rawar gani a aikin.

An fara tura kayan zabe jihohi

A wani labarin, kun ji cewa INEC ta ce ta riga ta fara raba kayayyakin zaɓen da ba su da alaƙa da ƙuri’a zuwa wasu jihohi gabanin babban zaɓen 2027.

Hukumar ta bayyana cewa rabon kayayyakin na daga cikin shirye-shiryen da take yi domin tabbatar da cewa komai ya kasance a shirye kafin lokacin gudanar da zaɓen.

Kwamishinan hukumar na ƙasa, Mohammed Haruna, ya ce za a kammala kai sauran kayan aiki da na’urorin BVAS da ba a raba ba zuwa jihohi kafin ƙarshen watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng