Tinubu Ya Jawo Wa Kansa Abun Magana da Ya Fadi Abun Kunyar da Ya Faru da Shi a Aso Rock

Tinubu Ya Jawo Wa Kansa Abun Magana da Ya Fadi Abun Kunyar da Ya Faru da Shi a Aso Rock

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na AAC a 2027, Omoyele Sowore, ya soki Tinubu bayan shugaban ƙasar ya bayyana cewa ya samu wata matsala a fadar shugaban ƙasa
  • Sowore ya ce masu ba shugaban ƙasa shawara ya kamata su gaya masa ya yi murabus idan gwamnatinsa ba za ta iya tabbatar da samar da ruwa a Aso Rock ba
  • Tinubu ya bayyana cewa an samu matsalar ne ranar Larabar da ta gabata, lokacin da yake aske gemunsa, yayin da ya halarci taron addu'a a Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar African Action Congress (AAC) a zaɓen 2027, Omoyele Sowore, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan katsewar ruwan da aka samu a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Sowore ya bayyana lamarin a matsayin gazawar magance wata muhimmiyar buƙata ta more rayuwa a cibiyar gwamnatin Najeriya.

Sowore ya soki Shugaba Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na AAC, Omoyele Sowore Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Abin da Sowore ya ce kan Tinubu

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a daren Lahadi, 22 ga watan Nuwamban 2026, ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin bil'adama ya ce ya kamata masu ba Tinubu shawara su gaya masa ya yi murabus.

Ya bayyana cewa bai kamata a samu matsalar samar da ruwa a fadar shugaban ƙasa ba, wadda ita ce cibiyar gudanar da harkokin gwamnatin tarayya.

Sowore ya rubuta cewa:

“Ba ka iya tabbatar da ci gaba da samar da ruwa a fadar Aso Rock ba, amma mutanen da ke tafa muku suna nuna cewa ba sa ƙaunar Najeriya.
“Ya kamata su gaya maka kai tsaye cewa idan ba za ka iya tafiyar da samar da ruwa a Aso Rock ba, to ka yi murabus. Mutanen nan marasa kunya ne.”

Yadda Tinubu ya bayyana katsewar ruwan

Martanin Sowore ya biyo bayan bayanin da Tinubu ya yi cewa an samu katsewar ruwan sha a fadar shugaban ƙasa ranar Larabar da ta gabata, lokacin da yake aske gemunsa.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamban 2026 yayin wani taron addu'a na musamman da iyalansa suka shirya a ƙungiyar Yoruba Tennis Club da ke Onikan, a jihar Legas.

Yayin da yake ba da labarin abin da ya faru, mai girma Bola Tinubu ya ce katsewar ruwan na daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta tun bayan zamansa a fadar shugaban ƙasa.

Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi aiki wajen magance gibin da ake da shi a fannin samar da ababen more rayuwa a Najeriya.

Tinubu ya yi magana a Legas
Tinubu na jawabi a wajen taron addu'ar da 'yan uwansa suka shirya masa a Legas Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sowore ya magantu kan lafiyar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya jaddada zargin da ya yi a baya cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da lafiya.

Sowore, wanda ya shahara a harkokin gwagwarmaya da kare hakkin dan adam, ya yi ikirarin cewa Tinubu ba shi da karfi da lafiyar ci gaba da jagorantar kasa kamar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng