Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani game da Matar da Ake Zargin Sarkin Daura Ya Taɓa Jikinta
Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, na fuskantar suka da tambayoyi daga jama'a bayan wata mata ƴar ƙasar waje, Mirka Cze, ta zarge shi da cin zarafinta ta hanyar taɓa jikinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Matar, wacce ta zo Najeriya yawon bude ido ta zargi Sarkin Daura ta taba mata wwuraren da ba su dace ba kuma na tare da izininta ba yayin ziyarar da ta kai fadarsa a Jihar Katsina.

Source: Instagram
Leadership ta ruwaito vewa zargin ya fito fili ne bayan matar ta kammala rangadin kwanaki 30 da ta yi a Najeriya.
Yadda akw sukar Sarkin Daura
Lamarin ya jawo martani daga sassa daban-daban, musamman a Arewacin Najeriya, inda ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama, malaman addinin Musulunci da sauran fitattun mutane suka buƙaci a gudanar da bincike.
Cze ta wallafa wani bidiyo na ganawarta da sarkin a shafukan sada zumunta, inda ta yi zargin cewa ya taɓa jikinta ba daidai ba duk da ta nuna rashin amincewarta.
Yayin da Majalisar Masarautar Daura ta ce tana nazarin bidiyon domin tantance sahihancinsa, batun ya ci gaba da tayar da muhawara kan ɗabi'un sarakunan gargajiya, haƙƙin mata da martabar masarautu a Arewa.
Abubuwa 7 game da Mirka Cze
Legit Hausa ta tattaro muku muhimman abubuwa guda bakwai da ya kamata ku sani game da Mirka Cze da zargin da take wa Sarkin Daura.
1. Ƴar yawon buɗe ido ce
Mirka Cze matafiyiya ce ƴar ƙasar waje wadda ta bayyana cewa asalinta yar ƙasar Poland ce, amma an haife ta a Jamhuriyar Czech.
An fi saninta a Instagram da sunan @beduinqa, inda take wallafa bayanai da hotunan tafiye-tafiyenta, abubuwan da take gani a al'adu daban-daban da kuma abubuwan ban sha'awa da take fuskanta a ƙasashe da dama.
2. Ta ziyarci ƙasashe 185
Mirka Cze ta kasance mai yawan fita ywon bude ido kuma ta ziyarci ƙasashe da dama a faɗin duniya.
Rahotanni sun nuna cewa ta ziyarci ƙasashe 185 daga cikin ƙasashe 197 da ta lissafa a matsayin wuraren da take son zuwa ko ta ziyarta.
Tafiye-tafiyenta sun haɗa da ƙasashe da dama a Afirka, Gabas ta Tsakiya da Asiya. A shafinta na sada zumunta, tana wallafa abubuwan da ta gani a ƙasashe irin su Yemen, Chadi da Comoros, da sauran wurare.
3. Najeriya ce ƙasa ta 184 da ta ziyarta
Najeriya na cikin ƙasashen da Cze ta ziyarta a yayin tafiye-tafiyenta na duniya. A tsawon kwanaki 30 da ta yi tana yawon buɗe ido a Najeriya, ta ziyarci wurare da dama a faɗin ƙasar.
Daga cikin biranen da ta ziyarta akwai Legas, Calabar, Ibadan, Benin City, Abeokuta, Osogbo, Ilorin, Abuja, Jos, Bauchi, Kano, Zariya, Katsina da Daura.
4. Ta ziyarci fadar Sarkin Daura

Kara karanta wannan
Zargin cin zarafi: Sarkin Daura ya shiga matsala bayan yaɗuwar bidiyonsa a Intanet
Cze ta yi zargin cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 14 ga Nuwamban 2026, lokacin da ta kai ziyara fadar Sarkin Daura a Jihar Katsina.
A cewarta, an shigar da ita wani ɗaki mai kayan alatu, inda ta zauna tare da sarkin suka tattauna game da tafiye-tafiyenta da kuma tarihin garin Daura.
Ta ce ganawar ta fara ne cikin yanayi mai kyau, amma daga baya abubuwa suka sauya har ta fara jin rashin daɗi, cewar rahoton Vanguard.

Source: Facebook
5. Ta zargi sarkin da taɓa jikinta
A cikin bayanin da ta wallafa a Instagram, Cze ta yi zargin cewa sarkin ya riƙe hannunta yana wasa da shi yayin da suke tattaunawa.
Ta ƙara da cewa ya rungume ta, ya sumbaci kumatunta, sannan daga baya ya taɓa ƙirjinta ba tare da izininta ba.
Ta ce ta sha nuna rashin amincewarta, inda ta riƙa cewa: “Sarki, a'a, a'a, a'a, a'a. Sarki, ba za ka riƙa taɓa ni haka ba.”
A cewarta, sarkin ya yi dariya duk da ƙin amincewar da ta nuna. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da zarge-zargen ta hanyar bincike mai zaman kansa ba.
6. Ta ɗauki bidiyon da tabaran Meta
Cze ta yi iƙirarin cewa ta yi amfani da tabarau na zamani na Meta mai ɗaukar bidiyo wajen yin rikodin ganawar da ta yi da sarkin.
Ta ce ta kunna na'urar ne bayan ta fara jin rashin jin daɗi sakamakon taɓawar da ta yi zargin sarkin ya yi mata.
Daga baya bidiyon ya bazu sosai a shafukan sada zumunta, lamarin da ya jawo kiraye-kirayen neman gudanar da bincike kan abin da ya faru.
7. Lokacin da ta wallafa bidiyon
Matar ta bayyana cewa ta yanke shawarar fito da zargin a bainar jama'a ne bayan ta kammala rangadin kwanaki 30 da ta yi a Najeriya tare da barin ƙasar.
Ta ce ta ji daɗin zagayawa Najeriya, haɗuwa da mutane da ziyartar wurare daban-daban, amma ta bayyana ganawar da ta yi a fadar Sarkin Daura a matsayin abin da ya tayar mata da hankali.
Ta kuma nuna cewa watakila ba ita ce mace ta farko da ta fuskanci irin wannan hali ba, duk da cewa har yanzu babu wata hujja mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirari.

Kara karanta wannan
Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai

Source: Facebook
An goge bidiyon matar da Sarkin Daura
Kun ji cewa ƴar ƙasar waje da ta zargi Sarkin Daura da taɓa jikinta ba tare da izininta ba ta tabbatar da cewa an cire bidiyonta daga shafin Instagram.
Matar ta bayyana cewa ta nemi a sake duba matakin da Instagram ya ɗauka na cire bidiyon, inda ta buƙaci a gudanar da bincike domin tantance ko matakin ya dace.
Asali: Legit.ng


