Gwamnatin Legas ta haramta sana'ar Achaba da tuka adaidaita a kananan hukumomi 6
Gwamnatin jihar Legas ta haramta sana'ar tuka babur mai kafa biyu, watau 'Achaba', da babur mai kafa uku, da aka fi sani da 'adaidaita', a fadin kananan hukumominta guda shidda (LCDAs).
Kananan hukumomi 6 da sabuwar dokar da shafa sune kamar haka; karamar hukumar Apap da Apapa Iganmu, Lagos Mainland da Yaba LCDA a karamar hukumar Surelere, Itire-Ikate da Coker Aguda LCDAs, karamar hukumar Ikeja da Onigbongbo da Ojodu LCDAs.
Sauran sune; karamar hukumar Eti-Osa, Ikoyi-Obalende da Iru/Victoria Island LCDAs, karamar hukumar Lagos Island da Lagos Island ta gabas LCDA.

Asali: Twitter
A cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin, gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa dokar zata fara da karfinta daga ranar 1 ga watan Fabrairu, 2020.
Gwamnatin jihar ya bayyana cewa daukan wanna mataki yana daya daga cikin tsare-tsarenta na tsaftace hanyoyin cikin garin Legas da kuma kare jama'a daga illolin da wadannan hanyoyin sufuri (Achaba da adaidaita) ke haifar wa.
DUBA WANNAN: 'Ra'ayinka bai dameni ba' - Buhari ya mayar wa da TY Danjuma martani
Sabuwar dokar na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar KAROTA mai kula da cunkuson ababen hawa a cikin birnin Kano ke kokarin rage yawan baburan adaidaita sahu da suka mamaye manya da kananan titunan birnin garin.
Kimanin kusan shekaru goma kenan da haramta sana'ar Achaba a birnin Kano.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng