Rashin Imani: Yan Bindiga Sun Rutsa Bayin Allah Suna Barci, Sun Bude Masu Wuta

Rashin Imani: Yan Bindiga Sun Rutsa Bayin Allah Suna Barci, Sun Bude Masu Wuta

  • An kashe aƙalla makiyaya huɗu, sannan ’yan bindiga suka yi awon gaba da shanu sama da 100 bayan kai hari a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato
  • Ƙungiyar Coalition of Fulani Registered Organisations ta ce an kashe ko raunata mambobinta 95 tsakanin Afrilu da Nuwamba 2026
  • Ƙungiyar ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro su tabbatar da adalci da kariya ga kowa ba tare da nuna bambancin ƙabila ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - An kashe aƙalla makiyaya huɗu, yayin da ’yan bindiga suka yi awon gaba da shanu sama da 100 bayan sun kai hari wata rugar Filani a Ƙaramar Hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne a daren Lahadi, lamarin da ya ƙara tayar da hankula kan sake barkewar hare-hare a kan al’ummomin makiyaya a jihar.

Kara karanta wannan

Matawalle ya raba motoci 1000 za su shiga lunguna nemawa Tinubu kuri'u

Filato
Taswirar jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ƙungiyar Coalition of Fulani Registered Organisations ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai a Jos, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ta yi gargaɗi kan abin da ta kira hare-hare da kashe-kashe da kuma lalata kadarorin mambobinta ba kakkautawa.

Shugaban ƙungiyar na jihar, Garba Abdullahi, ya ce an kashe ko raunata mambobinta 95 sakamakon hare-haren da aka kai musu tsakanin Afrilu da Nuwamba 2026.

Ya kuma bayyana cewa an sace ko kashe shanu 1,240 a cikin wannan lokaci, yayin da aka ƙone ko rusa gidaje sama da 22.

A cewarsa, hare-haren sun kuma jawo lalata kadarori masu daraja, ciki har da motoci, babura, injinan ban ruwa da sauran kayayyaki da darajarsu ta kai miliyoyin Nairori.

An tabbatar da sabon hari

Da yake tabbatar da sabon harin, shugaban ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) na Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya ce maharan sun shiga garin ne lokacin da mazauna yankin suke barci.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Babayo ya nuna damuwa kan ci gaba da kai wa makiyaya hare-hare, inda ya ce ana kashe mambobinsu tare da lalata hanyoyin da suke dogaro da su wajen neman abinci.

“Abin da ke faruwa da mutanenmu yana damunmu. Ana kashe mu tare da kai mana hari a kullum. Kiwo shi ne hanyar samun abin rayuwarmu, amma ana hana mu yin hakan,” in ji shi.

Ya kuma yi zargin cewa wasu mutane sanye da kayan jami’an tsaro sun shiga al’ummomin Fulani tare da aikata laifuka daban-daban, amma ba a hukunta su.

Shugaban MACBAN ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya shiga tsakani domin magance matsalar tsaron.

Ya kuma nuna damuwa kan abin da ya kira sintirin jami’an tsaro mai nuna bambanci a al’ummomin Fulani, inda ya yi zargin cewa jami’an tsaron suna ziyartar matsugunansu ne kawai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262