Garin neman kiba: Sojojin da ta gayyata don zane makwabcinta sun hallaka kanwarta

Garin neman kiba: Sojojin da ta gayyata don zane makwabcinta sun hallaka kanwarta

Wata mata mai shekaru 25 mai suna Onyeka Nwachukwu ta kira wasu sojoji biyu don su zane makwabcinta mai suna Nelson Jackson, ta fada cikin mummunan tashin hankali. A halin yanzu tana garkame a wajen adana mutane na rundunar ‘yan sandan jihar Legas bayan sojojin sun kashe kanwarta mai suna Chinwendu Nwachukwu.

Jaridar The Punch ta gano cewa, tsautsayin ya faru ne a ranar talata a rukunin gidaje na Seasida dake Badore a yankin Ajah dake jihar Legas.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Bala Elkana ya bayyanawa jaridar The Punch cewa Onyeka ta samu hatsaniya ne da Jackson. Elkana yace a yayin wannan tashin hankalin ne ta kira mazan biyu da ake zargin sojoji ne don ladabtar mata da Jackson.

A fadan da aka yi mazan suka yi harbi wanda harsashin ya kashe Chinwendeu a take.

DUBA WANNAN: APC na da kyakyawar makoma a Kudu maso gabas - Ohanaeze

Elkana ya kara da cewa, harsashi ya samu mahaifiyar Jackson mai suna Ego Onyekwelu, amma bata mutu ba.

Yace, “Anyi fada tsakanin Onyeka Nwachukwu da makwabcinta Nelson Jackson. A hakan ne Onyeka ta gayyato wasu maza biyu da ake zargin sojoji ne don su ladabtar da Jackson.”

A wannan halin ne harsashin da suka harba ya samu ‘yar uwar Onyeka mai suna Chinwendu mai shekaru 30 inda ta mutu a take. Harsashin ya samu mahaifiyar Jackson amma ta raunata ne. Tuni sojojin suka tsere daga inda abun ya faru. A nan suka bar bindiga kirar Pistol wacce ‘yan sandan suka samu tare da harsasai uku.” Cewar Bala Elkana.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yace tuni suka kama Onyeka da Jackson a yayin da aka mika matsalar zuwa sashin bincike na musamman na manyan laifuka da ke Yaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel