Wata daliba ta fadi sumammiya a kotu bayan ta ga wanda ya ci zarafinta

Wata daliba ta fadi sumammiya a kotu bayan ta ga wanda ya ci zarafinta

A ranar Laraba ne wata daliba da bukatar sakaya sunan ya gifta, ta fadi ta suma a gaban wata kotun laifukan cin zarafi dake jihar Legas bayan hada ido da tayi da wani mutum da yayi mata fyade, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a lokacin da alkalin ya bukaci ganin mai makarantar Apex School dake Ajah, jihar Legas a gaban kotun. Fitowar Fasto Timothy ke da wuya yarinyar mai shekaru 19 ta fasa ihu tare da rintse idanuwanta. Daga baya kuwa sai faduwa tayi kasa warwas.

Dalibar mai matsalar ido da kuma nakasa kadan, ta fadi ne bayan da tayi arba da Onyiriuka mai shekaru 45 a duniya.

Mai shari'a Abiola Soladoye ne ya lallabi dalibar a kan ta kwantar da hankalinta. Tuni alkalin ya bada hutun sa'a daya don a samu hankalin yarinyar ya kwanta. "Zaki iya bayar da shaidarki idan hankalinki ya kwanta. Mun bada hutun sa'a daya." cewar mai sharia'r.

"Kada ki damu, Ubangiji na tsare da ke kuma kotu na tsare da ke," cewar alkalin.

Bayan hutun sa'a daya, an dawo cigaba da jin kara a gaban kotun, kuma wani ma'aikacin ma'aikatar shari'a ta jihar ya kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari kafin su dawo cikin dakin kotun.

DUBA WANNAN: Yadda 'yan uwan mara lafiya suka yi wa likita mace zigidir a Abuja

Matashiyar mai shekaru 19 ta samu jagorancin lauyanta mai suna Arinola Momoh-Ayokanbi, wanda ya bayyana zargin Onyiruika da ake da yi wa yarinyar fyade a lokacin da take da shekaru 13 a duniya.

"Nasan shi, sunansa fasto Timothy kuma yayi lalata dani. Ya kaini gidansa har sau uku inda ya bude wandonsa tare da saka min mazakutarsa a gabana. Ya taba zuwa gidanmu yayi lalata dani kuma ya rike bulala cewa idan na sanar da wani zai zane ni kuma ya kashe ni. Sunan makarantar Apex School kuma faston mu ne," cewar matashiyar.

Kamar yadda matashiyar ta bayyana, mahaifiyarta ta kama faston yana lalata da ita a wata rana, lamarin da yasa mahaifiyarta ta mika kokenta ga rundunar 'yan sandan jihar.

Mai shari'a Abiola Soladoye ya dage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu.

Faston na fuskantar zargin lalata yarinyar ne tun shekaru 6 da suka gabata. Wannan laifin abin hukuntawa ne da zaman gidan yari na tsawon rayuwa, kamar yadda sashi na 137 ya tanadar na jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel