Magana Ta Kare: Jam'iyyar Adawa Ta Yanke Shawara, Ta Umarci Mabiyanta Su Zabi Tinubu a 2027

Magana Ta Kare: Jam'iyyar Adawa Ta Yanke Shawara, Ta Umarci Mabiyanta Su Zabi Tinubu a 2027

  • Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya miƙa wa Shugaba Bola Tinubu tutar jam’iyyar APGA don nuna goyon bayanta ga takararsa a zaɓen 2027
  • Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya karɓi tutar a madadin Tinubu yayin taron yakin neman zabe a Awka
  • Soludo ya ce bai kamata Kudu maso Gabas ya ci gaba da ware kansa daga manyan harkokin siyasar ƙasa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra, Nigeria - Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya miƙa tutar jam’iyyar APGA ga Shugaba Bola Tinubu a hukumance.

Hakan ya nuna cewa APGA ta amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar da za ta marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Shettima.
Gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo lokacin da ya tarbi mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima
Source: Facebook

Gwamna Soludo ya mika wa Tinubu tuta

Vanguard ta rahoto cewa an gudanar da bikin miƙa tutar ne a dandalin Alex Ekwueme da ke Awka, yayin babban gangamin siyasa mai taken “SoluTinubu 2027."

Kara karanta wannan

Rikicin APC a jihar Kano ya yi ƙamari, an aika saƙon gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya karɓi tutar a madadin Tinubu.

Da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar da shugabannin siyasa a wurin gangamin, Soludo ya ce wannan mataki na nufin ƙoƙarin shigar da yankin Kudu maso Gabas cikin manyan harkokin siyasar ƙasa.

Gwamnan ya ce:

“Muna wakiltar APGA ne, kuma muna miƙa tutar jam’iyyarmu ga Shugaban ƙasa.”

Soludo ya ja hankalin al'ummar Igbo

Ya buƙaci mazauna Anambra su sake nazarin yadda suke zaɓe a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ya tuna cewa Tinubu ya samu kashi 0.8 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a jihar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Soludo ya ce gangamin ya biyo bayan makonni da jam’iyyarsa ta kwashe tana gudanar da tarukan tattaunawa da al’umma a faɗin jihar, waɗanda ya bayyana a matsayin tattaunawa kan haɗin kan al’ummar Igbo da ci gabansu.

Da yake amincewa da cewa akwai korafe-korafe da ra’ayoyin siyasa daban-daban a yankin Kudu maso Gabas, ya ce yankin ba zai iya ci gaba da ware kansa daga harkokin siyasar ƙasa ba.

Kara karanta wannan

"Ba sai an yi magudi ba," Gwamna ya ce an kammala zaben shugaban kasa na 2027

Gwamnan ya yi tambaya da cewa:

“A tsarin dimokuraɗiyya, wane tasiri muke da shi ban da ƙuri’unmu da haɗin gwiwa da sauran ƙasar nan? Wane amfani muke samu idan muka sake ɓarnatar da ƙuri’unmu?”
Tinubu da Soludo.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo a fadar Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya bayar da hujjar cewa goyon bayan shugaban ƙasa daga Kudu domin ya kammala wa’adin mulki na shekara takwas kafin a mayar da mulki Arewa zai bai wa Kudu maso Gabas damar samun ƙarin tasiri a siyasa.

Gwamnan ya kuma bayyana amincewarsa da takarar Tinubu da Shettima, yana mai cewa babu wani ɗan takarar adawa da ya gabatar da sahihin zaɓi na daban da ya yi daidai da manufofin tattalin arziki da ci gaban da gwamnatin ke bi.

Soludo ya hango nasarar Tinubu

Kun ji cewa gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya bukatar maguɗin zaɓe domin samun wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

Gwamna Soludo ya ce alamu sun nuna cewa APC ta yi wa yan adawa fintinkau, kuma za ta sake lashe zabe cikin sauki a shekara mai kamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262