Rotimi Amaechi ya ce ba za su iya karasa aikin dogon Legas a Afrilu ba

Rotimi Amaechi ya ce ba za su iya karasa aikin dogon Legas a Afrilu ba

Ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi, ya fito ya ce da kamar wuya a gama aikin titin jirgin kasan da ake yi daga Legas zuwa Ibadan.

Rotimi C. Amaechi ya bayyanawa Manema labarai cewa har yanzu akwai tulin aikin da ya kamata ace an yi, amma ba a iya kammalawa ba.

Ministan ya bayyana wannan ne lokacin da ya kai ziyara inda ake aikin a Ibadan domin ya kewaya ya ga inda ‘yan kwangilan su ka kwana.

A bara Ministan ya yi alkawari za a kammala wannan aiki a Watan Afrilun shekarar 2020, kuma har a kaddamar da aikin a cikin Watan Mayu.

Amaechi ya na tare da Karamar Ministarsa, Gbemisola Saraki, da kuma gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde wajen wannan zagaye da ya zo ya yi.

KU KARANTA: Buhari: Ba shinkafa ta sa na rufe iyakokin shiga Najeriya ba

Rotimi Amaechi ya ce ba za su iya karasa aikin dogon Legas a Afrilu ba
Rt. Hon. Rotimi Amaechi ya ce aikin Legas-Ibadan ba zai kammalu ba
Asali: Facebook

“Ganin yadda yanayin aikin ya ke a Apapa, kammala shi a Watan Afrilu ba mai yiwuwa bane, musamman bangaren dogon da tashar ruwa.”

“Akwai rushe-rushe da za mu yi; dole za mu ci karo da layin mai har a bangaren tashar ruwa, amma layin Agege zuwa Ibadan sumul ya ke.”

“Dayan kwangilar ta taso ne daga Ebute-Metta zuwa tashar ruwan Apapa wanda ya kai kilomita shida, a nan ne mu ke samun matsaloli.”

“Idan ku na bin wannan aiki, za ku san mun saba samun matsala da Legas saboda yanayin cinkoson garin.” Inji Rotimi Amaechi.

“A game da wa’adin Afrilu, ba zan iya amsa wannan tambaya ba, Idan ku ka tambaye su (‘Yan kwangila), za su fada maku cewa gaskiya ne.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel