Tashin hankali: Saurayi yayi kokarin yankewa mahaifiyarsa gaba, saboda taje tana zina da wasu a titi

Tashin hankali: Saurayi yayi kokarin yankewa mahaifiyarsa gaba, saboda taje tana zina da wasu a titi

- Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta damke wani mutum mai suna Joshua mai shekaru 22

- Matashin yayi yunkurin yanke gaban mahaifiyar shi ne bayan ya zargeta da yawon banza

- Ya ce tana tozarta shi da bashi kunya kuma bata mutunta kanta, don haka zai fi idan ya cire gaban nata dugurungun

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta damke wani mutum mai suna Joshua Adetutu mai shekaru 22 bayan da yayi yunkurin yanke gaban mahaifiyar shi saboda zargin ta da yake da bin maza.

Kamar yadda Gistmania ta ruwaito, lamarin ya faru ne a titin Odobanjo kusa da titin Gwamna da ke yankin Ikotun a jihar Legas inda mahaifiyar matashin ke zama da mahafiyarta.

An gano cewa Joshua ya garkame mahaifiyar shi a daki ne tare da dauko wuka don aiwatar da nufin shi. Ya tureta kasa ne tare da yunkurin yanke gabanta.

Amma kuma Jennet ta samu taimakon makwabtansu wadanda suka cece ta tare da kiran 'yan sandan yankin Idimu da ke Legas.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sanya matan Hausawa ke tsufa da zarar sunyi aure

An kama Joshua tare da garkame shi. A yayin da 'yan sanda ke tambayar shi, Joshua ya zargi mahaifiyar shi da tozarta shi tare da bashi kunya kuma bata mutunta kanta a yankin.

Jennet ta yi aure ne inda ta haifa Joshua da sauran 'ya'yanta kafin ta rabu da mahaifinsu don rayuwa ita kadai. Da farko dai Joshua na zama da mahaifinshi amma sai ya damfareshi kuma yayi zaman gidan yari na Badagry. Jennet ce ta dinga fafutukar fito da Joshua kuma ya fara rayuwa tare da ita a wajen mahaifiyarta.

A nan ne ya gane cewa mahaifiyar shi na yawan samun baki maza wadanda ya zarga da lalata da ita. Don haka ne ya yanke hukuncin yanke gaban ta baki daya, lamarin da ya kai shi hannun 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: