CP: ‘Yan Sanda sun karbe Babura 188 da Keke Napep 78 a Jihar Legas

CP: ‘Yan Sanda sun karbe Babura 188 da Keke Napep 78 a Jihar Legas

Bayan dabbaka sabuwar dokar haramta amfani da babur da keke-napep a wasu Yankunan Legas, jami’an tsaro sun damke wadanda su ka sabawa doka.

Labari ya zo mana daga Jaridar Vanguard cewa bayan shigo da wannan doka ta hana Acaba, ‘Yan Sanda sun kama mutane 40, tare da rika abubuwan hawan.

Babura 188 ne su ka shiga hannun ‘Yan Sanda a Legas. Bayan haka an karbe keke-napep a sakamakon haramta amfani da su a wasu wurare a jihar.

Gwamnatin Babajide Sanwo-Olu ta zabi wasu kananan hukumomi da ta haramtawa amfani da babura da keke-napep a kokarin gyaran da ta ke yi a Garin.

A Ranar Asabar, Kwamishinan ‘Yan Sandan Legas, Hakeem Odumosu, ya baza Dakaru domin su yi maganin wadanda su ka sabawa wannan doka a yankunan.

Gwamnati ta ce wannan doka ta fara aiki ne a farkon Ranar 1 ga Watan Fubrairu. Gwamnatin Legas ta hana Acaba watau Okada da kuma hayar Keke-Napep.

KU KARANTA: An mutu wajen rikicin 'Yan Acaba da Jami'an tsaro a Legas

CP: ‘Yan Sanda sun karbe Babura 188 da Keke Napep 78 a Jihar Legas
An daina haya da Babura da keke-napep masu kafa uku a Legas
Asali: Twitter

Hakeem Odumosu ya nuna gamsuwarsa game da yadda wannan doka ta fara aiki a cikin kananun hukumomin da aka dabbaka su, tare da godewa jama’an Gari.

Daga yanzu duk wanda aka samu yana Okada ko aikin Keke zai jawowa kansa fushin hukuma. 'Yan Sanda su na ta karbe abubuwan hawan tare da kama masu aikin.

Daga cikin wadanda ake kamawa a jihar har da masu babura da motocin da ke cikin Tawagar muhimman mutane na VIP, wadanda ba su dauke da takardun lamba.

Babu lokacin da aka halattawa Masu haya aiki a bangarorin na Legas, don haka ‘Yan Sanda su ka ce wannan doka ta na aiki a kowane lokaci kuma a kan kowane a jihar.

CP Odumosu ya sake tabbatarwa mutanen Legas cewa babu wanda ya fi karfin doka. A jawabinsa, Kwamishinan ‘Yan Sandan ya sha alwashin casa masu sabawa doka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng