Damfara: Kotu ta bukaci a bawa Fashola masauki a gidan gyaran hali

Damfara: Kotu ta bukaci a bawa Fashola masauki a gidan gyaran hali

Wata kotun laifuka na musamman ta Ikeja a ranar Talata ta bada umarnin tsare Lere Fashola, mashiryin Esquire Nigerian Legal Awards a gidan gyaran hali a kan zarginsa da ake da damfarar kadara ta naira miliyan 20.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa Fashola, lauya ne kuma mawallafin mujallar Esquire Law, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gurfanar da Fashola ne tare da kamfaninsa mai suna Legal Blitz Ltd a kan laifuka uku da suka hada da damfara.

Bayan musanta aikata laifin da yayi, Mai shari’a Sherifat Solebo ta bada umarnin tsaresa a gidan gyaran hali. Mai shari’a Solebo ba ta sanar da gidan gyaran halin da za a adana mata Fashola ba.

Kotu ta bukaci a bawa 'Fashola' masauki a gidan gyran hali
Kotu ta bukaci a bawa 'Fashola' masauki a gidan gyran hali
Asali: UGC

“Kafin ji da yanke hukuncin bukatar belin wanda ake zargin, ina umartar da a adana min shi a gidan gyaran hali,” cewar Solebo.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai wa fasinjojin jirgin kasa hari a Kaduna

Kamar yadda EFCC ta bayyana, an kama lauyan ne bayan Adeyemi Adebola ya kawo kararsa a kan karyar da yayi wajen karbar masa naira miliyan 20 yayin siyen wata kadara.

Kadarar na nan a fuloti mai lamba 732, Block XXVII (27), Omole Residential Scheme, Phase 2, Isheri, Legas.

EFCC ta zargi cewa wanda ake zargin ya waskar da kudin har naira miliyan 20 ne wanda mai koken ya tura masa don siyen kadarar

Mai shari’a Solebo ta dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu don sauraron bukatar belin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel