Labarin Sojojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta karrama jami’ai da sojojin Operation Lafiya Dole su 37 sakamakon hakazakarsu wajen yaki da ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar.
Hedkwatar rundunar sojin ruwa ta sanar da mutuwar tsohon Shugaban hafsoshinta, Vice Admiral Patrick Seubo Koshoni mai ritaya. Legit.ng ta ruwaito cewa an bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu a wani jawabi.
Sai kuma gashi a ranar Alhamis shugaba Buhari ya kira wani taro na gagga wa da shugabannin rundunonin tsaro na kasa a fadarsa, lamarin da yasa wasu suke zargin cewa taron ba zai rasa nasaba da kiran neman Buhari ya yi murabus ba.
Shugaban kungiyar CHRSJ, Adeniyi Sulaiman ya sake hurowa Buhari wuta ya tsige Shugabannin Sojojin Najeriya saboda matsalar harkar tsaro.
Shugaban Majalisar Dattawa watau Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya yarda akwai matsalar tsaro. Ahmad Lawan da Osinbajo sun koka da halin da ake ciki a Najeriya.
A makon jiya mu ka ji cewa NSCDC ta bukaci ayi bincike a kan kisan Ndubuisi Emenike bayan Jami’in tsaron ta ya kashe ‘Dan siyasa a Imo.
Kwanan nan aka hana wasu ‘Yan Mata fita zuwa kasashen waje haka kurum. Abin da ya sa NIS ta ki barin su shiga jirgi shi ne lalata su ke neman zuwa su yi a waje.
A jiya Mahaifin Leah Sharibu ya yi magana game da rade-radin haihuwar ‘Diyarsa. Sharibu cikin fushi, yake cewa ban yarda ‘Diyata ta auri ‘Dan Boko Haram har sun haihu ba.
Dazu nan Gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola ya maidawa MURIC raddi kan batun Kiristantar da Amotekun. Gwamnan ya yi kaca-kaca da kungiyar MURIC ne dazu.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari