Gwamnan Zamfara Ya Yi Magana kan Kama Dan Ta'adda Bello Turji

Gwamnan Zamfara Ya Yi Magana kan Kama Dan Ta'adda Bello Turji

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi magana kan matakan da suke dauka wajen magance matsalar tsaro da ta addabi Najeriya
  • A jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ce suna cigaba da kokari domin kawo karshen dukkan 'yan ta'addan da ake ganin kamar sun gagara
  • Da aka masa tambaya game da kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji, Mai girma gwamnan ya bayyana cewa suna daukar matakin kama shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - Yayin da batun rashin tsaro ke kara kamari a Najeriya, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ce suna kokarin shawo kan matsalar.

Ya yi magana game da dan ta'addan da ya yi suna wajen kama mutane a Zamfara, Bello Turji, inda ya ce ana cigaba da farautar shi.

Kara karanta wannan

Ran Rarara ya baci da aka soki Tinubu kan tsaro, ya zargi Davido da bata Najeriya

Bello Turji da Dauda Lawal
Bello Turji a hagu da Gwamna Dauda Lawal a dama. Hoto: Sulaiman Bala Idris|Zagazola Makama
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da BBC Hausa da tashar ta wallafa a Facebook, Dauda Lawal ya ce ba komai game da tsaro ake bayyana wa a duniya ba.

Ana sa ran a kama Bello Turji

Yayin da aka yi masa tambaya ko cewa akwai wasu 'yan ta'adda sun gagari gwamnati, Dauda Lawal ya ce babu wanda ya fi karfin hukuma.

Game da cewa Bello Turji ya gagari hukuma, Dauda Lawal ya ce:

"Wallahi bai isa ba, babu wani dan ta'adda da ya gagari gwamnati, lokaci ne kawai kuma in shaa Allahu shi kan shi za mu same shi."

Da aka tambaye shi ko yaushe za su kama Bello Turji, gwamnan ya kara da cewa:

"Ba za a iya ba da lokaci ba, ai yaki dan zamba ne, amma bisa matakan da muke dauka, in shaa Allah lokaci ne, zai zo hannu."

Game da kama 'yan ta'adda

Kara karanta wannan

Kungiyar musulmi ta goyi bayan mafitar da Matawalle ya kawo kan matsalar tsaron Najeriya

Gwamnan ya tabbatar da cewa ya samar da askarawa a jihar, tare da kawo yan sa kai daga Borno da kuma sojoji da 'yan sanda domin yaki da 'yan bindiga.

A kan haka aka tambaye shi kan rashin kutsawa dazuka su kama 'yan bindiga lura da cewa ya taba cewa sun san maboyar 'yan ta'ddan.

Dauda Lawal ya mayar da amsa da cewa a halin yanzu ma irin aikin da suke yi a Zamfara kenan domin murkushe dukkan masu garkuwa da mutane.

Gwamna Dauda Lawal
Dauda Lawal na addu'a a ofis. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Source: Twitter

Ya kara da cewa sun kama da yawa daga cikin 'yan ta'addan, wasu na hannun hukuma wasu kuma sun riga sun tafi lahira.

A karshe, Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta cigaba da kokarin da ta ke domin kawo zaman lafiya a Zamfara.

Ga bayanin da Dauda Lawal ya yi a kasa:

Maganar Rarara kan rashin tsaro

A wani labarin, kun ji cewa mawakin jam'iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara ya yi kira ga jama'a da su daina ruruta matsalar rashin tsaro a kafafen sadarwa.

Rarara ya bayyana cewa yawan magana kan wadanda aka sace ko daura biyon su a intanet na kara jefa su cikin hadari a hannun masu garkuwa.

Ya buga misali da abin da ya faru da shi, inda ya ce a lokacin da Atiku Abubakar ya yi magana bayan sace mahaifiyar shi, ta kara shiga cikin matsala a daji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng