Buhari ya sake sayo ma rundunar Sojan sama sabbin jiragen yaki (Hotuna)
Rundunar mayakan Sojan kasa ta sanar da amsan wasu sabbin jiragen yaki guda biyu da kirar, Agusta 109 Power Attack, da gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sayo musu.
Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, inda yace a yanzu haka injiniyoyin rundunar suna harhada jiragen don rantsar dasu a ranar 27 ga watan Afrilu.
KU KARANTA: Aikin ashsha! Yadda Uwargida ta halaka Maigidanta da wuka a jahar Kebbi
Kaakaki Daramola yace babban hafsan Sojan sama, Air Marshal Saddique Abubakar ne ya tabbatar da shigo da jiragen biyu yayin da yake jawabi a bikin liyafar cin abinci daya shirya ma dakarun rundunar Soja same dake yaki da Boko Harama a garin Maiduguri, don murnar bikin Easter.
Saddique ya bayyana cewa duba da irin gudunmuwar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke baiwa rundunar, tare da hadin kan majalisar dokokin kasar, yana sa ran zasu cigaba da samun sabbin kayan aiki, tare da samar da horo ga jami’ansu.
Sadiqque ya shirya wannan liyafar ce a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu a garin Maidugurin jahar Borno, inda aka ci abinci mai rai da lafiya tare da nama iya nama, aka kuma sha kayan shaye shaye da tande tande, sa’annan aka nishadantu da dadadan wakokin bare bari.
Kaakakin ya kara da cewa Saddique na amfani da wannan dama don gode ma Sojojinsa, tare da jinjina musu bisa kokarin da suke yi wajen yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas, sa’annan yace irin wanna taro na dauke ma Sojojin kewar rashin iyalansu a kusa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng