Babban hafsan Sojan sama ya nishadantar da Sojojin dake yaki da Boko Haram (Hotuna)
Babban hafsan rundunar mayakan Sojan sama, Air Marshal Saddique Abubakar ya shirya ma zaratan dakarun Sojin saman Najeriya dake fafatawa a filin daga na jahar Borno, liyafar cin abinci tare da nishadantar dasu.
Sadiqque ya shirya wannan liyafar ce a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu a garin Maidugurin jahar Borno, inda aka ci abinci mai rai da lafiya tare da nama iya nama, aka kuma sha kayan shaye shaye da tande tande, sa’annan aka nishadantu da dadadan wakokin bare bari.
KU KARANTA: Zaratan Sojoji sun kashe yan bindiga 6, sun kama dakatai 2 masu aikin leken asiri
Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a ranar Litinin, inda yace Saddique na amfani da damar irin wannan liyafa don ganawa da dakarun Sojinsa a duk lokacin da ake wani sha’anin biki, don haka ya shirya musu wannan saboda bikin Easter da kiristoci ke yi.
Kaakakin ya kara da cewa Saddique na amfani da wannan dama don gode ma Sojojinsa, tare da jinjina musu bisa kokarin da suke yi wajen yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas, sa’annan yace irin wanna taro na dauke ma Sojojin kewar rashin iyalansu a kusa.
Haka zalika baya ga Sojojin da suka halarci liyafar, rundunar ta gayyaci al’umma unguwar Gomari, unguwar da sansanon rundunar Sojan sama take zuwa wannan liyafa, inda kuma dayawansu suka amsa kira, suka ci, suka sha, suka yi nak!
Daga karshe kaakaki Daramola yace rundunar ta gudanar da irin wannan liyafar cin abinci a sansaninta dake Yola, da kuma sansaninta dake jahar Katsina.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng