Zaratan Sojoji sun tafka ma Boko Haram ta’asa, sun kashe mayaka 39

Zaratan Sojoji sun tafka ma Boko Haram ta’asa, sun kashe mayaka 39

Rundunar hadaka ta kasashen dake makwabtaka da Najeriya, sun samu gagarumar nasara akan mayakan kungiyar Boko Haram a wata karan batta da suka kwasa a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu, inda suka kashe yan ta’adda akalla 39.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito anyi wannan dauki ba dadi ne a daidai wani wuri da ake kira da suna Cross Kaura dake jahar Borno a lokacin dda mayakan Boko Haram suka kaddamar da hari akan Sojojin, amma reshe ya juye da mujiya.

KU KARANTA: Ruwa baya tsami banza: An kama jami’in Soja cikin wasu gungun masu garkuwa da mutane

Zaratan Sojoji tafka ma Boko Haram ta’asa, sun kashe mayaka 39
Zaratan Sojoji tafka ma Boko Haram ta’asa, sun kashe mayaka 39
Asali: Facebook

Kaakkain rundunar hakadan ta MNJTF, Kanal Timothy Antigha ne ya tabbatar da wannan nasara, inda yace suna cigaba da gudanar da aikin da suka yi ma taken ‘Yancin Tafki’ a yankin tafkin Chadi, inda yace sun kashe yan ta’adda da dama tare da kwace tarin makamai.

Sai dai sanarwar ta kara da cewa akwai Sojoji guda ashirin da suka samu raunuka daga harbe harben bindiga, inda yace tuni sun daukesu da jirgi zuwa asibiti domin su samu kulawar data dace.

A wani labarin kuma Dakarun rundunar Sojan na musamman sun tarwatsa wasu gungun yan bindiga da suka kaddamar da hare hare a kauyukan Rafi da Dola dake cikin lardin Mada na karamar hukumar Gusau ta jahar Zamfara a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.

Kaakakin rundunar, Komodo Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru, inda yace sun samu bayanai dake nuna yan bindigan sun fara tattaruwa a kauyukan Rafi da Dola da nufin kai musu hari, hakan tasa suka garzaya don fafatawa dasu.

Daramola ya cigaba da fadin ba tare da bata lokaci ba suka tura da wasu rukunin dakarun Sojoji na musamman, wanda suka tarwatsa shirin yan bindiga, har ma suka kashe guda biyu daga cikinsu, yayin da sauran suka ranta ana kare dauke da munanan raunuka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel