Ba hutu: Buhari ya sake gana wa da shugabannin hukmomin tsaro, ya basu sabon umarni (Hotuna)

Ba hutu: Buhari ya sake gana wa da shugabannin hukmomin tsaro, ya basu sabon umarni (Hotuna)

- A cigaba da kokarinsa na kawo karshen aiyukan ta'addanci a fadin Najeriya, musammam jihar Zamfara, shugaba Buhari ya gana da shugabannin hukumomin tsaro

- A cewar Gabriel Olanisakin, shugaban rundunar tsaro, ya ce shugaba Buhari ya basu umarnin cewar kar su nuna tausayi a kan 'yan ta'adda

- Shugabannin rundunonin sojojin sama, kasa da na ruwa da shugaban rundunar 'yan sanda da takwaransa na hukumar tsaro ta farinkaya sun halarci taron

A cigaba da kokarin kawo karshen aiyukan ta'addanci a yankin arewa maso yamma, musamman jihar Zamfara, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake gana wa da shugabannin hukumomin tsaro a fadar sa da ke Abuja.

Shugabannin rudunonin sojan sama, kasa da na ruwa da shugaban rundunar 'yan sanda na kasa (IGP) da takwaransa na hukumar tsaro ta farin kaya sun halarci taron domin gabatar da jawabi ga shugaba Buhari a kan yanayin tsaro da kuma kalubalen da suke fuskanta.

Ba hutu: Buhari ya sake gana wa da shugabannin hukmomin tsaro, ya basu sabon umarni (Hotuna)
Buhari da Buratai
Asali: Twitter

Ba hutu: Buhari ya sake gana wa da shugabannin hukmomin tsaro, ya basu sabon umarni (Hotuna)
Fitowar shugabannin hukmomin tsaro bayan gana wa da Buhari
Asali: Twitter

Da yake gana wa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsu, ta tsawon fiye da sa'a biyu, da shugaba Buhari, shugaban rundunar tsaro ta kasa, Janar Gabriel Olanisakin, ya bayyana cewar shugaban kasa ya basu umarni su nuna rashin tausayi wajen murkushe 'yan bindigar jihar Zamfara da ragowar 'yan ta'adda a sassan kasa.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da kashe N1.3bn don biyan hakkin ma'aikatan da suka mutu

Yanzu haka an kaddamar da wasu sabbin atisaye da suka hada da Harbin Kunama III, Dirar Mikiya, Sharen Daji da 'Puff-Adder' domin kawo karshen aiyukan ta'addanci a yankin arewa maso yamma da ragowar sassan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel