'Yan bindiga sun kai hari jihar Jigawa

'Yan bindiga sun kai hari jihar Jigawa

- Wasu 'yan bindiga da ba a san daga ina suke ba sun kai wani mummunan hari wani kauye a jihar Jigawa

- Mun samu rahoton 'yan bindigar sun kashe mutane masu yawan gaske sannan sun jikkata da dama a kauyen

Mun samu rahoton wasu 'yan bindiga sun kai wani muummunan hari kauyen Abaya da ke kan hanyar Wurma a karamar hukumar Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

'Yan bindigar, da su kai harin kauyen a jiya Laraba, sun harbe mutane kusan talatin.

Har yanzu dai ba a tabbatar da ainihin mutanen da abin ya shafa ba.

'Yan bindiga sun kai hari jihar Jigawa

'Yan bindiga sun kai hari jihar Jigawa
Source: Twitter

Bayan haka, rahotanni sun nu na cewa an kashe da yawa daga mutanen garin, sannan wasu da yawa suma sun samu raunika.

Matsalar 'yan bindiga da masu satar mutane ta yi kaurin suna a Najeriya, musamman a yankin jihar Borno, Katsina, Zamfara, Kaduna, Niger da Abuba.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin rataye wasu mutane guda 7

Sai kuma ga wani abin mamaki jihar Jigawa ta na daya daga cikin jihohin da ba a fiya samun matsalar tsaro ba a yankin arewa, sai gashi kuma jiya 'yan ta'addar sun bulla a yankin.

Nan ba da jimawa ba za mu kawo muku cikakken rahoton halin da ake ciki a jihar ta Jigawa akan matsalar 'yan bindigar da su ka bullo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel