Mazraoui: Dan Kwallon Manchester zai Koma Ajin Kur'ani don Ya Dawo Limami

Mazraoui: Dan Kwallon Manchester zai Koma Ajin Kur'ani don Ya Dawo Limami

  • Dan wasan Morocco da ke Manchester United Noussair Mazraoui ya ce yana son haddace Alƙur’ani kuma ya zama limami bayan ya bar ƙwallon ƙafa
  • Yayin wani bayani da ya yi, Noussair Mazraoui ya bayyana cewa rayuwa 'yar kadan ce kuma zai iya ajiye kwallon kafa bayan gasar kofin duniya ta 2026
  • Wasu rahotanni sun nuna cewa tun yana kungiyar kwallo ta Bayern Munich yake bayyana burinsa na zama mahaddacin Alƙur’ani a rayuwar shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Morocoo - Yayin da ake ci gaba da gudanar da gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026, ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Morocco, Noussair Mazraoui ya nuna shawa'ar komawa haddar Kur'ani.

Noussair Mazraoui da a halin yanzu ke taka leda a Manchester United, ya sha yabo daga mutane da dama bayan ya bayyana wani buri da ya zarce harkar ƙwallon ƙafa, wato haddace Alƙur’ani da kuma zama limami.

Kara karanta wannan

Yadda aka nemi ceto malamar Islamiyya amma mutane suka taru suka kashe ta

Noussair Mazraoui a filin wasa
Noussair Mazraoui yayin gasar cin kofin duniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

'Dan jarida da ya shahara da tattara labarai game da kwallon kafa, Fabrizio Romano ne ya wallafa labarin Mazraoui a shafinsa na Facebook.

'Dan kwallon Man Utd zai dawo limami

'Dan kwallon Mazraoui ya nuna sha'awar kom awa harkokin addini ne da yake magana bayan ya wakilci tawagar ƙasar Morocco a gasar cin kofin duniya ta FIFA da ake gudanarwa a halin yanzu a Amurka, Canada da Mexico.

Ya bayyana cewa yana tunanin wata rayuwa ta daban bayan ya bar harkar ƙwallon ƙafa, inda aka ruwaito, ya ce:

“Wataƙila zan yanke shawarar yin ritaya bayan gasar cin kofin duniya. Rayuwa gajera ce. Ina son haddace Alƙur’ani kuma wata rana in zama limami a masallaci.”

Wannan furuci ya yi tasiri sosai a tsakanin Musulmai a sassa daban-daban na duniya, lura da cewa ya fito ne daga cikin fitattun 'yan kwallo a duniyar yau.

Noussair Mazraoui
Noussair Mazraoui yana takawa Man United leda. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya yi batun haddar Kur'ani a baya

Kara karanta wannan

Abin mamaki: 'Yan ta'adda sun tara mutanen gari, sun yi masu wa'azi a jihar Neja

Shafin Islam on Web ya wallafa cewa ba wannan ne karon farko da Mazraoui ke magana kan alaƙarsa da Alƙur’ani ba.

A lokacin da yake taka leda a Bayern Munich, ya bayyana a kafafen sada zumunta cewa yana da burin zama mahaddacin Alƙur’ani.

Ya ce wannan tunani ya zo masa ne bayan ya ji bai gamsu da yadda yake karatun Alƙur’ani a sallah ba, domin ya haddace ƙananan surori kaɗan ne kawai.

Da yake da niyyar ƙarfafa dangantakarsa da Alƙur’ani, Mazraoui ya nemi taimakon wani malami mai suna Sheikh Ayyub, wanda ya fara taimaka masa wajen haddace Alƙur’ani, inganta karatunsa da fahimtar ma’anoninsa.

Messi ya kafa sabon tarihi a ƙwallo

A wani labarin, Legit ta kawo muku cewa Lionel Messi ya kafa tarihin yawan cin kwallaye mafi yawa a gasar cin kofin duniya ta FIFA.

Rahotanni sun nuna cewa hakan ya faru ne bayan da ya zura kwallon farko ta ƙasarsa a wasan rukuni na J da suka buga da Austria.

Zura kwallon da ya yi ya kai jimillar kwallayen Messi zuwa 18 a cikin gasar cin kofin duniya guda shida da ya halarta a tarihin rayuwarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng