'Yan ta'addar jihar Zamfara sun fara kaura suna shiga wasu jihohi

'Yan ta'addar jihar Zamfara sun fara kaura suna shiga wasu jihohi

Gwamnan jihar Osun ya bukaci hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya da su sanya ido akan 'yan ta'addar jihar Zamfara, wadanda yanzu ake tunanin sun fara canja sheka daga jihar Zamfara suna shiga wasu jihohin

A ranar Alhamis dinnan ne da ta gabata, gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya bukaci jami'an tsaro da sarakunan gargajiya da su lura sannan kuma su dakile duk wani shiri na 'yan ta'addar jihar Zamfara, wadanda suke yin kaura daga jihar suna komawa wasu jihohi.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da babban sakatarensa a fannin sadarwa ya fitar, Mista Adeniyi Adesina, bayan gwamnan ya yi magana a wurin wani taro, akan gudanar da tsarin tsaro, wanda sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomin tsaro, kungiyoyin jama'a, 'yan siyasa, 'yan kasuwa da sauransu suka hallata a Osogbo.

'Yan ta'addar jihar Zamfara sun fara kaura suna shiga wasu jihohi
'Yan ta'addar jihar Zamfara sun fara kaura suna shiga wasu jihohi
Asali: Depositphotos

Oyetola ya ce "ya zama wajibi a sanya matakan da za su magance matsalar 'yan ta'adda da ke faruwa a jihar Zamfara shigowa jihar Osun."

Gwamnan ya jaddada bukatar tabbatar da tsaro ta hanyar tattara bayanai, sannan sarakunan gargajiya su saka ido a yankunansu da kuma bukatar a fadakar da jami'an tsaro su sanya ido wurin dakile duk wani shiri na ta'addanci a jihar.

Gwamnan da kuma jami'an tsaro sun gargadi masu bada gidajen haya, akan bai wa mutane wadanda ba su da kyakkyawar masaniya a kansu.

KU KARANTA: An kama karuwai sama da 30 a Abuja

"Idan ka bawa mutumin da baka san shi ba hayar gida, kuma muka gano cewa dan ta'adda ne, to duk abinda ya biyo baya kai ka jawowa kan ka," in ji Oyetola.

Ya bukaci sarakunan gargajiya da su yi aiki tukuru, domin masu hakar ma'adanai suna nan suna yawo a wasu yankuna na cikin jihar."

Gwamnatin tarayya ta hana hakar ma'adanai a jihar Zamfara, bayan ta samu bayanan cewa 'yan ta'addar jihar su na da alaka da masu hakar ma'adanai wadanda ba su da lasisi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel