Sojan sama ya mutu yayin basu horon diro wa daga jirgi

Sojan sama ya mutu yayin basu horon diro wa daga jirgi

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da mutuwar wani jami'inta mai mukamain Corporal, Meshach Iliya Komo, yayin basu horon diro wa daga jirgin yaki.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da darektan yada labarai da hulda da jama'a, Daramola, ya fitar a yau, Lahadi.

NAF ta mika sakon ta'aziyya ga iyalin marigayin bisa rashin jami'in sojin.

"Rundunar sojin na mai bakin cikin sanar da mutuwar daya daga cikin jami'anta, Corporal Meshach Iliya Komo, wanda ya mutu yau, 14 ga watan Afrilu, 2019, a Kaduna, bayan afkuwar hatsari yayin basu horon diro wa daga jirgi.

"A madadin rundunar sojin sama, shugaban rundunar, Air Marshal Sadique Abubakar, na mika sakon ta'aziyya ga iyalin marigayin bisa rashin da suka yi. Mu na masu addu'ar Allah ya ji kansa," a cewar jawabin.

Sojan sama ya mutu yayin basu horon diro wa daga jirgi

Sojan sama ya mutu yayin basu horon diro wa daga jirgi
Source: Twitter

Ko a kwanakin baya bayan nan, Legit.ng ta kawo maku labarin cewar rundunar sojin sama dake aikin tabbatar da tsaro a jihar Borno tayi babban rashi bayan fankar jirginsu na yaki mai saukar ungulu tayi sanadiyar mutuwar wani babban jami'in soja mai mukamin 'air chief marsahal' da aka bayyana sunasa a matsayin Umar.

DUBA WANNAN: An kama 'yan sanda 5 a Legas bayan sun harbe wata budurwa mai shekaru 20 da wani mutum

Wani daga cikin matuka jirgin da abin ya faru a kan idonsa ya shaidawa jaridar TheCable cewar lamarin ya faru ne a garin Bama a yammacin ranar Asabar, 6 ga watan Afrilu.

Hakan ta faru ne bayan jirgin ya samu matsala.

Marigayin, wanda ya kasance daya daga cikin matuka jirgin, ya fita ne domin dauko jakarsa, amma yayin da yake wuce wa ta jikin fankar jirgin sai ta fille masa kai, kuma nan take ya fadi matacce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel