Trump Ya Kawo Tsarin da Kayan Abincin Amurka zai Rika zuwa Iran

Trump Ya Kawo Tsarin da Kayan Abincin Amurka zai Rika zuwa Iran

  • Shugaba Donald Trump ya ce mashigar Hormuz a bude take gaba daya a yanzu kuma ana cigaba da jigilar man fetur ta cikin ta
  • Donald Trump ya bayyana cewa ana samun ci gaba a tattaunawar Iran tare da gargadin kada a karya yarjejeniya a nan gaba
  • Game da kudin Iran da za a mika, shugaba Trump ya ce za a takaita amfani da su ne wajen sayen abinci daga manoman Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - A cikin wasu jerin bayanai da ya gabatar, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da abubuwan da suka shafi cinikayya, tsaron harkokin jiragen ruwa da kuma tattaunawar diflomasiyya da ake yi da Iran.

Yayin da yake kokarin nuna komai na tafiya yadda ya kamata, Trump ya tabbatar da cewa masu shiga tsakani na samun nasarar matsawa gaba wajen cimma cikakkiyar yarjejeniya.

Kara karanta wannan

Iran ta yi sabuwar matsaya kan Hormuz bayan gama zama da Amurka

Shugaban Amurka a wajen wani taro
Shugaba Donald Trump a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Roya News ta wallafa cewa Donald Trump ya yi magana ne bayan Iran da Amurka sun yi tattaunar kai tsaye a Switzerland.

Maganar bude mashigar Hormuz

Babban abin da shugaban ya mayar da hankali a kai shi ne dawo da harkokin zirga-zirgar jiragen ruwa masu muhimmanci ta Hormuz.

Trump ya bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba wajen tabbatar da tsaron jigilar kayayyaki ta ruwa, yana mai cewa Amurka ta samu damar jigilar man fetur fiye da yadda take yi a baya.

"Mashigar Hormuz a bude take gaba daya,"

In ji Trump, yana mai karawa da cewa:

"Iran na gudanar da abubuwa yadda ya kamata dangane da mashigar Hormuz."

Trump ya jaddada cewa tsarin tattalin arzikin diflomasiyya da yake aiwatarwa a halin yanzu zai hana tabarbarewar tattalin arzikin duniya.

Ya tabbatar wa kasuwanni da jama'a cewa hanyar da yake bi wajen tafiyar da al'amuran Iran ba za ta janyo koma bayan tattalin arzikin duniya ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Iran ta yi watsi da tattaunawa da Amurka kan makamai masu linzami

Shugabannin kasar Iran a wajen taro
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran za ta saye hatsin Amurka

A wani sabon tsari da ya shafi sassauta takunkumi, Trump ya bayyana wata hanya mai tsauri ta yadda za a tafiyar da kudin Iran da aka rike.

Shugaban ya ce duk wasu kudim Iran da za a sako ba za a ba su a matsayin kudi kai tsaye ba. Maimakon haka, za a sanya amfani da su kai tsaye da bangaren noma na Amurka.

"Kudin Iran da aka daskarar da za a sako za a yi amfani da su ne kawai wajen sayen abinci daga manoman Amurka,"

In ji Trump.

Sai dai duk da maganar da Trump ya yi, Jerussalem Post ta wallafa cewa shugabannin Iran sun ce hakan ba zai taba yiwuwa ba.

Iran ta tattauna da Amurka

A wani labarin, mun kawo muku cewa Qatar da Pakistan da ke shiga tsakani sun yi magana bayan zaman Amurka da Iran a Switzerland.

Kara karanta wannan

A karshe, Trump ya amince Iran ta mallaki makamai masu karfin gaske

Kasashen biyu da ke shiga tsakani sun bayyana cewa an samu gagarumar nasara a zaman kai tsaye da aka yi a zagayen farko.

Sun sanar da cewa an tattauna game da abubuwa da dama da suka hada da mashigar Hormuz da hare-haren Isra'ila a Lebanon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng