Zamfara: Rundunar sojin sama ta yiwa 'yan bindigar jihar Zamfara luguden wuta

Zamfara: Rundunar sojin sama ta yiwa 'yan bindigar jihar Zamfara luguden wuta

- Rundunar sojin saman Najeriya ta samu nasarar kashe samada 'yan bindiga 10 a dajin Sububu da ke jihar Zamfara

- Rundunar ta ce da yawa daga cikin 'yan bindigar sun arce cikin daji da munanan raunika jikinsu

A jiya ne rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da cewa dakarunta na rundunar 'Operation Diran Mikiya' sun kashe 'yan bindiga sama da 10 a dajin Sububu da ke cikin jihar Zamfara.

Kakakin rundunar sojin saman, Air Commodore Ibikunle Daramola, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya yi, inda ya ce lamarin ya faru ranar Litinin 22 ga watan Afrilu, 2019, ya kara da cewa rundunar ta yi amfani da jirgin yaki guda biyu da kuma jirgi mai saukar ungulu guda daya domin taimakawa mayakan da wuraren da 'yan ta'addar suke a dajin Sububu, da kuma dajin Dumburum da kewaye wadanda ke cikin karamar hukumar Shinkafi.

Zamfara: Rundunar sojin sama ta yiwa 'yan bindigar jihar Zamfara luguden wuta
Zamfara: Rundunar sojin sama ta yiwa 'yan bindigar jihar Zamfara luguden wuta
Asali: Depositphotos

Ya ce jiragen yakin sun sun kai wa 'yan ta'addar hari inda suka samu nasarar kashe sama da mutane 10 daga cikin su, inda wasu daga cikin su suka tsere da munanan raunuka a jikinsu.

Matsalar tsaro dai a jihar Zamfara taki ci taki cinyewa, duk kuwa da irin kokarin da hukumomin tsaron Najeriya ke yi wurin kawo karshen 'yan bindigar a yankin.

KU KARANTA: Sarkin Kano ya ba da wasu dalilai da ya sa Najeriya ba za ta taba gyaruwa ba

A cikin watan nan ne gwamnatin tarayya ta saka dokar rufe duk wasu wuraren tona ma'adanai a wasu yankuna dake arewacin kasar nan, inda ta bayyana yin hakan da wasu bayanan sirri da ta ke samu da ke nuna cewa 'yan bindigar da suka hana mutane sakat a wasu jihohi a kasar nan, ana zargin masu hakar ma'adanai ne wadanda ba su da lasisi.

Bayan haka kuma rundunar sojin saman Najeriya ta yi zargin cewa akwai hadin bakin sarakunan gargajiya a ta'addancin da ke faruwa a yankin jihar Zamfara, sai dai kuma sarakunan jihar sun fito sun karyata ikirarin da hukumar sojin ta ke yi inda suka bukaci hukumar ta bayyana wadanda suke da hannu a cikin ta'addancin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel