An yi karon batta tsakanin 'yan ta'adda da 'yan kungiyar sa kai a Katsina

An yi karon batta tsakanin 'yan ta'adda da 'yan kungiyar sa kai a Katsina

Da alama talakawan Najeriya sun fara gajiya da gafara sa ba su ga kaho ba, domin kuwa sun fara nuna alamun sun fitar da rai da jami'an tsaron Najeriya, saboda a yanzu haka sun fara hada gangami suna shiga cikin dazuka domin farautar 'yan ta'adda

Al'umma daga garuruwa da dama daga kananan hukumomin da suke makwabtaka da dajin Kamako ne suka hada wata runduna ta 'yan sa kai, inda suka hadu a garin Dungun Ma'azu dake cikin karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina, inda suka shiga dajin na Kamako domin yin dauki ba dadi da 'yan bindigar da su ke addabar garuruwan na su.

Wani wanda aka yi abun a gabanshi ya shaidawa manema labarai cewa, akalla mutane sama da 500 ne suka yi tururuwa daga kananan hukomin jihar ta Katsina dama wasu bangarori na jihar Kaduna, inda suka nufi wannan daji don kawo karshen 'yan ta'addar.

An yi karon batta tsakanin 'yan ta'adda da 'yan kungiyar sa kai a Katsina
An yi karon batta tsakanin 'yan ta'adda da 'yan kungiyar sa kai a Katsina
Asali: Original

Mutumin wanda bai bayyana sunansa ba, ya ce anyi dauki ba dadi sosai tsakanin 'yan ta'addar da kuma 'yan kungiyar sa kan.

Ya bayyana cewa 'yan kungiyar sa kan sun kashe 'yan ta'addar akalla mutane 40, sannan kuma an kashe 'yan kungiyar sa kan guda 21.

KU KARANTA: Buratai ya yi alkawarin inganta rayuwar sojojin Najeriya

Mutumin ya ce harin da 'yan kungiyar sa kan suka kai ya yi matukar tasiri, saboda koda suka koma wurin da safe 'yan ta'addar duk sun gudu.

Mutumin ya ce ganin hakan nema yasa 'yan kungiyar sa kan suka sake zage dantse, sannan suka kara daura damara, sannan kuma wasu mutanen suka dinga tururuwa suna shiga kungiyar, domin aje ayi dauki ba dadin da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel