Zargin Kashe Kashe: Masarautar Zamfara ta nemi yafiyar rundunar sojin sama

Zargin Kashe Kashe: Masarautar Zamfara ta nemi yafiyar rundunar sojin sama

Masarautar jihar Zamfara ta nemi gafarar rundunar hukumar sojin saman Najeriya, sakamakon zargin ta da kashe al'ummar jihar wadanda ba su ji ba kuma ba su gani yayin wani luguden wuta da ta zartar wajen yakar 'yan ta'adda.

Rundunar sojin sama

Rundunar sojin sama
Source: Twitter

Ciyaman na masarautar Zamfara da ya kasance Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad, shi ne ya nemi wannan gafara yayin da wata kungiyar mutum bakwai ta manyan dakarun sojin sama ta ziyarci fadar sa da ke garin Anka a ranar Asabar bisa jagorancin AVM Idi Lubo.

Kwanaki kadan da suka gabata Sarakunan gargajiya na jihar Zamfara sun yi zargin cewa harin da rundunar sojin sama ta zartar kan sansanin miyagun 'yan ta'adda ta hanyar luguden wuta da jiragen yaki na samam ya salwantar da rayukan wasu al'ummomi na jihar da ba su ji ba kuma ba su gani ba.

Sarkunan kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito sun bayyana hakan ne da sanadin Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru yayin ganawar sa da menama labarai.

KARANTA KUMA: Macizai sun hana shugaban kasar Liberia aiki a ofishin sa

Furucin Sarakunan ya biyo bayan wani taron gaggawa da suka gudanar domin tattauna batutuwa kan zargin da Ministan Tsaro na kasa Mansur Dan Ali ya yi da cewar wasu daga cikin Sarakunan na da hannu cikin goyon bayan ci gaba da aukuwar ta'addanci a jihar Zamfara.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar 'yan sandan Najeriya ta samu nasarar cafke wasu miyagun ababe arba'in masu ta'addancin garkuwa da mutane a jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel