Babu gagararre sai bararre: Yadda mayakan Sojan sama suka halaka yan bindiga

Babu gagararre sai bararre: Yadda mayakan Sojan sama suka halaka yan bindiga

Rundunar Sojan sama ta sanar da cewa mayakanta sun samu nasarar halaka yan bindiga guda dai dai har guda ashirin da biyar a jahar Zamfara, yayin da ta jikkata wasu da dama a wasu hare hare data kaddamar musu da jiragen yakinta.

Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka, inda yace Sojojin sun kai wannan hari ne a karkashin aikin Operation Diran Mikiya bayan samun bayanan sirri game taruwar yan bindiga a sansaninsu dake Ajia.

KU KARANTA: Zafi zafi: Kasuwa ta bude ma masu sayar da kankara da ruwan sanyi a Kano

“Sojojin dake aikin Operation Diran MIkiya sun tarwatsa wani sansanin yan bindiga da suke taruwa don tsara hare harensu a kauyen Ajia, inda suka kashe yan bindiga guda 25.” Inji shi.

A cewar Ibikunle, yan bindigan suna amfani da wasu sansanoni a kauyukan Ajia da Wanoke a matsayin mafaka, dukkaninsu a cikin karamar hukumar Birnin Magaji na jahar Zamfara.

Inda ya kara da cewa rundunar ta tura wani jirgin yakin Najeriya kirar Alpha Jet zuwa wani gida da yan bindigan suka fakewa, inda jirgin ya tashi gidan gaba dayansa da bamabamai, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar yan bindiga da dama.

Cikin wani bidiyo da rundunar ta watsa a kafafen sadarwa, an hangi yadda jiragen yakin suka halaka wasu yan bindiga da suke tserewa a kafa suna neman mafaka, tare da lalata sansanonin nasu gaba dayansu, wasu kuma har kauyen Wanoke aka bi su kafin daga bisani aka halakasu.

Daga karshe kaakakin ya nemi jama’a dasu taimaka ma rundunar da duk wasu bayanai da zasu taimakesu a aikinsu, musamman wanda ya shafi motsin duk wasu mutane da basu yarda dasu ba, ko kuma yan bindiga.

A wani labarin kuma, dakarun rundunar Sojan kasa sun yi nasarar damko wuyar wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane daya dade yana addabar jama’an jahar Kaduna a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu.

Shi dai wannan mugun sunansa Sani Ibrahim Iliyasu Birtu, kuma bafillace ne, inda dakarun rundunar Sojan suka kamashi a dajin Rijana dake cikin karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel