Ranar kin dillanci: Jiragen yaki sun yi ma yan bindiga luguden wuta a dajin Zamfara

Ranar kin dillanci: Jiragen yaki sun yi ma yan bindiga luguden wuta a dajin Zamfara

Dakarun rundunar mayakan Sojan sama ta Najeriya sun yi amfani da jiragen yaki wajen yi ma taron yan bindigan jahar Zamfara ruwan wuta ta sama a wasu mabuyansu dake cikin dazukan jahar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Soja sama, Iya komodo Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka, inda yace Sojojin sun kai wannan hari ne a karshen makon data gabata bayan samun bayanan sirri dake tabbatar musu da taruwar yan bindiga a mafakokinsu.

KU KARANTA: Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da mahaifin wani Ciyaman har gida

“Sojojin dake aikin Operation Diran MIkiya sun tarwatsa wani sansanin yan bindiga da suke taruwa don tsara hare harensu a kauyen Ajia, hakan nan Sojojin sun kashe yan bindiga da dama a Ajia da Wonake, cikin karamar hukumar Birnin Magaji na jahar Zamfara.” Inji shi.

Kaakakin ya cigaba da cewa rundunar ta sake turawa da wani jirgin yakin Najeriya kirar Alpha Jet zuwa wani gida da yan bindigan suka fake a ciki, inda jirgin ya tashi gidan gaba daya ta hanyar jefa masa bamabamai, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar yan bindiga da dama.

Cikin wani bidiyo da rundunar ta watsa a kafafen sadarwa, an hangi yadda jiragen yakin suka halaka wasu yan bindiga da suke tserewa a kafa suna neman mafaka, wasu kuma har kauyen Wanoke aka bi su kafin daga bisani aka halakasu.

A wani labarin kuma wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da Mista Wellington Magbisa, mahaifin shugaban karamar hukumar Sagbama ta jahar Bayelsa, Honorabul Magbisa Michael.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 7 ga watan Afrilu ne yayin da suka dira gidansa da misalin karfe 12 na dare a unguwar Mile 2 cikin garin Sagbama, inda suka yi awon gaba dashi, kamar yadda kaakakin rundunar Yansandan jahar Taraba, Butswat Asinim ya tabbatar

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel