Sojoji za Su Fara Shiga Daji Yaki da 'Yan Bindiga tare da 'Yan Jarida

Sojoji za Su Fara Shiga Daji Yaki da 'Yan Bindiga tare da 'Yan Jarida

  • Rahoto ya nuna cewa gwamnatin tarayya na shirin bai wa 'yan jarida damar raka sojoji yayin wasu ayyukan soja dazuka domin su ga me ke faruwa
  • Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Mai ritaya) ne ya ce hakan zai inganta sahihan rahotannin tsaro da ƙara gaskiya a ayyukan soja
  • Christopher Musa ya ce haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da jami'an tsaro zai taimaka wajen fahimtar da jama'a halin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya na duba yiwuwar ƙaddamar da wani sabon tsari da zai bai wa 'yan jarida damar rakiyar sojoji yayin gudanar da wasu ayyuka.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalam ya sanya yada labaran karya cikin abu 2 da ke rura witar rashin tsaro

An bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin inganta rahotannin tsaro da kuma bai wa jama'a damar fahimtar ainihin halin da ake ciki wajen yaƙi da masu tayar da ƙayar baya da sauran ƙalubalen tsaro.

Janar Chiristopher Musa
Ministan tsaron Najeriya a lokacin da ya ke aikin soja. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa Ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ne ya bayyana haka a ranar Alhamis yayin taron koli kan tsaro da kungiyar 'yan jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya a Abuja.

Dalilin gayyatar 'yan jarida

Wanda ya wakilce shi, mai ba shi shawara na musamman, Rear Admiral Olusanya Bankole, ya ce wannan tsari da ake shirin aiwatarwa zai ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro.

Ministan ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa wajen fahimtar da jama'a game da ayyukan tsaro da zaman lafiyar ƙasa, yana mai cewa harkokin tsaro a yanzu sun wuce iyakokin fagen daga kawai.

Ya ƙara da cewa rikice-rikicen zamani na ƙara kasancewa masu tasiri ta fuskar bayanai da labarai, lamarin da ke sa kafafen yaɗa labarai zama muhimman masu ruwa da tsaki a tsarin tsaron ƙasar.

Kara karanta wannan

Maharazu Tsiga: Tsohon janar da 'yan bindiga suka taba sacewa ya ba da shawara kan tsaro

A cewarsa, bai kamata a auna nasarar ayyukan tsaro da nasarorin soja kaɗai ba, har ila yau ya kamata a yi la'akari da irin amincewar da jama'a ke da ita ga hukumomi.

Alakar soja da 'yan jarida

Ministan ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin ma'aikatar wajen ƙarfafa hulɗa da kafafen yaɗa labarai da tabbatar da cewa bayanan da suka shafi ayyukan soja suna isa ga jama'a.

Ya jaddada cewa kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin 'yan jarida da hukumomin tsaro za ta taimaka wajen ƙara yarda da hukumomi a tsakanin jama'a tare da inganta sakamakon ayyukan tsaro a ƙasa.

Jami'an tsaro da Christopher Musa
Christopher Musa da wasu manyan jami'an tsaron Najeriya. Hoto: Defence Headquaters
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa ana shirin aiwatar da wannan tsari ne a daidai lokacin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro da dama, ciki har da matsalar masu tayar da ƙayar baya.

An harbe dan bindiga a Edo

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Edo ta yi nasarar kama wani da ake zargi dan bindiga ne da ke garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

2027: Salon Peter Obi ya fita daban, ya bayyana tsare-tsarensa ga Najeriya

Rahotanni sun nuna cewa an kama wanda ake zargin ne bayan nasarar harbe wani mai garkuwa da mutane yayin musayar wuta da 'yan sanda.

Biyo bayan lamarin, gwamnan jihar ya bayyana cewa a shirye ya ke ya samar da kotu ta musamman domin hukunta masu garkuwa a Edo.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng