Matasan Arewa Sun Gano Abin da Ake Kullawa domin Sauke Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya

Matasan Arewa Sun Gano Abin da Ake Kullawa domin Sauke Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya

  • Kungiyar matasan Arewacin Najeriya ta Arewa Youth Assembly (AYA) ta ce wasu ’yan siyasa sun fara kulla-kullar sauke hafsoshin tsaro
  • Matasan sun yi zargin cewa wasu masu ruwa da tsaki sun gudanar da tarurruka a wata kasa ta Afrika domin cimma wannan buri
  • AYA ta bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ci gaba da mara wa hafsoshin tsaro baya domin dawo da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wasu matasan Arewacin Najeriya karkashin kungiyar Arewa Youth Assembly (AYA) sun bayyana damuwa kan abin da suka kira yunkurin sauke manyan hafsoshin tsaron kasa.

Matasan sun bayyana cewa ’yan siyasa sun fara yunkuri don cimma muradunsu na kifar da hafsoshin tsaron Najeriya a daidai lokacin da ake fama da matsalolin tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Rarara ya dawo da batun sace mahaifiyarsa, ya caccaki Atiku bayan Davido

Hafsoshi.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da hafsoshin tsaro jim kadan bayan wata ganawa a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Kungiya ta gano yunkurin sauke hafsoshin tsaro

Leadership ta rahoto cewa Mai magana da yawun kungiyar AYA na kasa, Aliyu Sanni Mohammed, ne ya bayyana hakan da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.

Ya ce kungiyar matasan ta san da cewa Najeriya na fuskantar manyan kalubalen tsaro da suka haddasa asarar rayuka da jefa iyalai cikin bakin ciki.

Sai dai ya ce ya kamata ’yan Najeriya su yaba da irin sadaukarwar da jami’an tsaro ke yi a kullum karkashin jagorancin hafsoshin tsaron da ke kan mulki.

Wa ke da ikon sauke hafsoshin tsaro?

Aliyu ya jaddada cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu cikakken ikon nadawa da sauke hafsoshin tsaro.

"Babu wani mutum, kungiya ko masu ruwa da tsaki da za su iya kwace wannan ikon da kundin tsarin mulki ya ba shugaban kasa," in ji shi.

Kara karanta wannan

An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya

Kungiyar AYA ta ce saboda haka bai kamata Shugaba Tinubu ya mika wuya ga matsin lamba daga kowace kungiya ko wani bangare ba.

AYA ta gano abin da ake shiryawa

Kungiyar ta ce ta samu bayanai da ke yawo cewa wasu masu fada a ji da ’yan siyasa masu neman iko sun gudanar da wasu tarurruka a wata kasa ta Afrika domin shirya yadda za a sauke hafsoshin tsaro.

Sai dai kungiyar ta bayyana cewa har yanzu wadannan zarge-zargen na bukatar cikakken bincike daga hukumomin da suka dace.

"Idan har da gaske akwai wasu da ke son amfani da shugabancin tsaro domin cimma muradun siyasa ko na kashin kansu, to wannan abu ne mai hadari kuma rashin kishin kasa ne," in ji Aliyu.
Shugaba Tinubu.
Mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana magana a wurin taro Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Kungiyar ta kuma yi kira ga Shugaba Tinubu da kada ya saurari masu kokarin haddasa sabani tsakaninsa da hafsoshin tsaro.

AYA ta kuma yi kira ga dukkan ’yan Najeriya ba tare da la’akari da kabila, addini ko jam’iyya ba su hada kai wajen tallafa wa jami’an tsaro, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi, shugabannin Kirista sun yi kira da murya daya kan matsalar tsaro

Majalisa ta taso hafsoshin tsaro gaba

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar wakilai ta tarayya ta bukaci hafsoshin tsaro su sauka daga mukamansu cikin mutunci idan ba za su iya yaye matsalar tsaro ba.

Majalisar ta kuma bukaci Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya fito da tsari mai karfi da zai kawar da 'yan bindiga, 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane.

Ta cimma wannan matsaya ne biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa da 'dan majalisa mai wakiltar Arochukwu/Ohafia, Hon. Ibe Osonwa, ya gabatar a zaman majalisar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262