Idan kaji ana ki gudu, sa gudu ne bai zo ba: Kalli yadda Sojoji suka kama shugaban masu garkuwa

Idan kaji ana ki gudu, sa gudu ne bai zo ba: Kalli yadda Sojoji suka kama shugaban masu garkuwa

Dakarun rundunar Sojan kasa sun yi nasarar damko wuyar wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane daya dade yana addabar jama’an jahar Kaduna a ranar Talata, 9 ga watan Afrilu.

Legit.ng ta ruwaito shi dai wannan mugun sunansa Sani Ibrahim Iliyasu Birtu, kuma bafillace ne, inda dakarun rundunar Sojan suka kamashi a dajin Rijana dake cikin karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna.

KU KARANTA: Zafi zafi: Kasuwa ta bude ma masu sayar da kankara da ruwan sanyi a Kano

Idan kaji ana ki gudu, sa gudu ne bai zo ba: Kalli yadda Sojoji suka kama shugaban masu garkuwa

Birtu
Source: Facebook

Sanin kowane cewa jahar Kaduna na fuskantar matsananci takura daga masu garkuwa da mutane, musamman a yankin Birnin Gwari da Giwa, da kuma babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, ga kuma kashe kashe a kudancin jahar.

A wani labarin kuma, babban sufetan Yansandan Najeriya, Muhammed Adamu ya kai ziyarar gani da ido jahar Zamfara don gane ma idanunsa irin wainar da ake toyawa a jahar biyo bayan sake ruruwan matsalar tsaro data dangancin ayyukan yan bindiga a jahar.

IG Adamu ya isa Gusau, babban birnin jahar Zamfara ne da misalin karfe 3 na ranar Talata, inda kai tsaya ya wuce taron masu ruwa da tsaki da rundunar Yansandan jahar ta shirya da al’ummar jahar.

A jawabinsa, IG Adamu yace makasudin ziyarar daya kawo shine tabbatar da an bi umarnin gwamnatin tarayya na dakatar da duk wasu ayyukan hakar ma’adanan kasa a jahar Zamfara gaba daya.

Abu na biyu daya kai shi jahar Zamfara shine jin ta bakin shuwagabannin gargajiya, shuwagabannin addinai, manoma, makiyaya da da sauran jama’a game da matsalar yan bindiga data addabi jahar.

Daga nan IG ya nemi goyon bayan masu ruwa da tsaki a jahar Zamfara ta wajen bayar da bayanan sirri ga hukumomin tsaro ta yadda zasu kawo karshen ayyukan miyagu a jahar, tare da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel