'Yan bindigar jihar Zamfara sun aika da wani sako ta wayar salula

'Yan bindigar jihar Zamfara sun aika da wani sako ta wayar salula

- 'Yan bindiga a jihar Zamfara sun aika da wani sako ta wayar salula

- 'Yan bindigar sun nuna cewa ba za a sake samun zaman lafiya ba har sai an janye jami'n tsaro a yankunan su

Shugaban 'yan ta'addar da suka addabi al'ummar jihar Zamfara ya bayyana cewa za su cigaba da kashe mutane a jihar, tunda har gwamnatin tarayya ta cigaba da aiko da jami'an tsaro domin dauki ba dadi dasu.

Ya bayyana hakan a wata hira da suka yi ta sirri da wani Sarki a jihar ta Zamfara, inda jaridar PUNCH ta samu rikodin din hirar da suka yi da Sarkin.

'Yan bindigar jihar Zamfara sun aika da wani sako ta wayar salula

'Yan bindigar jihar Zamfara sun aika da wani sako ta wayar salula
Source: Twitter

A hirar da suka yi da shugaban 'yan ta'addar, sun nuna rashin jin dadin su akan yadda gwamnatin tarayya ta ke aiko da rundunar tsaro domin kashesu, shugaban ya bayyana cewa hakan zai kara sanyawa su cigaba da tada hankalin al'ummar jihar.

Shugaban wanda ya yi magana da Sarkin, cikin harshen Hausa, ya ce ba za a taba samun zaman lafiya ba tunda har ku ka kira 'yan sanda, sojoji da sauran jami'an tsaro domin su dinga kashe mu.

KU KARANTA: Zamfara: Dakarun Soji sun kashe 'yan bindiga guda 7

Haka kuma wata majiya mai karfi ta yi zargin cewa Sarkin da suka yi waya da shugaban 'yan ta'addar, daya daga cikin sarakunan karamar hukumar Zurmi ne, wacce ke daya daga cikin kananan hukumomin da sake fama da rikici a jihar, sai dai kuma ba a bayyana sunan Sarkin ba har suka kammala wayar.

Ministan tsaro na tarayya, Mansur Dan Ali, ta ga bakin jami'in hulda da jama'a na shi, Col. Tukur Gusau, ya ce gwamnatin tarayya ta samu wani rahoto da ke da alaka da 'yan ta'addar jihar Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel