Sojoji sun yi ram da gungun masu garkuwa da mutane, sun ceto mutane 5 (Hotuna)

Sojoji sun yi ram da gungun masu garkuwa da mutane, sun ceto mutane 5 (Hotuna)

Sakamakon samun sahihan bayanan sirri game da wasu gungun barayin mutane da suka yi garkuwa da wani manajan gona, Gdowin Ugu a jahar Ondo, dakarun runduna ta 33 sun kai samame kauyen Jugbere dake cikin karamar hukumar Owo na jahar, inda yan barayin suke fakewa.

Legit.ng ta ruwaito Sojojin sun kaddamar da wannan sameme ne da misalin karfe 1 na daren Talata, inda suka kama barayi guda biyar, yayin da wasu barayi hudu suka tsere, sa’annan suka ceto mutane biyar da sukayi garkuwa dasu.

Sojoji sun yi ram da gungun masu garkuwa da mutane, sun ceto mutane 5 (Hotuna)
Sojoji sun yi ram da gungun masu garkuwa da mutane, sun ceto mutane 5 (Hotuna)
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rikici a Kannywood: Amina Amal ta nemi diyyar naira miliyan 50 daga wajen Hadiza Gabon

Daga cikin abubuwan da Sojojin suka gano a sansanin yan fashin akwai bindigar toka, adda, gatari, alburusai, wayar hannu da kuma zoben tsafi, a yanzu dai rundunar Sojin ta bayyana cewa zata mika miyagun ga hannun hukumar Yansanda.

Sojoji sun yi ram da gungun masu garkuwa da mutane, sun ceto mutane 5 (Hotuna)
Makamansu
Asali: Facebook

Da wannan ne kwamandan rundunar, Birgediya Janar ZL Abubakar yake baiwa jama’an jahar Ondo cewa a shirye suke su tabbatar da zaman lafiya, kare dukiyoyin da rayukansu, don haka ya umarci dakarun Sojoji su kara kaimi wajen gudanar da sintiri a jahar.

Haka zalika kwamandan ya nemi hadin kan al’ummar ta hanyar basu bayanai game da ayyukan miyagu a duk fadin jahar ta wasu lambobin waya kamar haka; 09030002151 da kuma 09030002161.

Sojoji sun yi ram da gungun masu garkuwa da mutane, sun ceto mutane 5 (Hotuna)
Sojoji sun yi ram da gungun masu garkuwa da mutane, sun ceto mutane 5
Asali: Facebook

A wani labarin kuma gwamnatin jahar Ondo, ta ware ma ofishin gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu naira miliyan goma sha uku (N13,000,000) don sanya katin kiran waya a kasafin kudin shekarar 2019.

Haka zalika an kasafta kudi naira miliyan dari biyar (N500,000,000) don tarbar manya baki da ake sa ran zasu halarci wasu muhimman bukukuwa ko taruka da gwamnatin jahar zata dauki nauyi a cikin shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng