Labaran Duniya
Yawancin shugabannin Afirka na yanzu suna cikin shearu 70s da 80s. Shugaba Muhammadu Buhari shine na shida a jerin takwas daga cikinsu, yana da shekaru 78.
Abdelkader Bensalah da Abdelaziz Bouteflika, dukkansu tsoffin shugabannin Algeria, sun mutu cikin mako guda. Dukkansu su biyun sun wuce shekaru ashirin a mulki.
Akwai wasu kasashe guda 6 a faɗin duniya da muka tattaro, waɗanda ake shafe dogon lokaci ana ganin hasken rana ba tare da duhun dare ya gitta ba kwata-kwata.
Wani jami’in dan sanda, Sajan Moses Kimenchu, ya ce wata budurwa ta yasar da shi bayan ya biya mata kudin makaranta. Matar ta kashe wayarta ta gudu daga gida.
Wani mijin yar Najeriya a ƙasar Italiya ya sheke matarsa har lahira a gaban abokan aikinta kuma a kamfanin da take aiki saboda ta nemi kotu ta raba aurensu.
Mace lamba ɗaya a ƙasar Amurka, Jill Biden, ta koma sana'arta ta koyarwa a wata kwaleji, ita ce matar shugaba ta farko da ta taɓa yin haka a tarihin matan.
Sojoji na musamman a ƙasar Guinea sun kifad da gwamnatin shugaba, Alpha Conde, Gwamnatin tarayya ta yi kira a gaggauta komawa mulkin demokaradiyya a ƙasar.
Babban limamin ƙasar Ghana, Sheikh Osman Nuhu Sharubutu, ya bada tallafin zunzurutun kuɗi dala dubu 10 ga kiristocin ƙasar domin su gina katafariyar majami'a.
Kungiyar Tarayyar Afirka a ranar Alhamis, 26 ga Agusta, ta nada tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a matsayin babban wakilin yankin gabashin Afirka.
Labaran Duniya
Samu kari