Arewa ba za ta iya yin nasarar jefa kuduncin ƙasar nan a yunwa ba

Arewa ba za ta iya yin nasarar jefa kuduncin ƙasar nan a yunwa ba

-A kwanan bayana nan ne dai wasu daga cikin al'ummar Arewa suka yi iƙirarin daina kayan kayan abinci Kudancin ƙasar nan.

-Sai dai kuma an samu wani farfesa wanda ke ganin cewa wannan takunkumi ba zai iya wa ƙudancin komai ba.

-Ya kawo misalai da na yadda wasu shugabanni suka riƙa goyon bayan Fulani makiyaya.

Jaridar the Tribune ta rawaito farfesa Abiodun Salahu na jami'ar North-West da ke Afirka ta kudu ya bayyana cewa ƙoƙarin hana isar da kayan abinci kudancin ƙasar nan daga Arewa abu ne da bai zai je ko'ina ba.

Ya bayyana hakan ne ga jaridarTribune a ranar Asabar kan rahoton da ke nuna cewa mutanen Arewa, da ke tare motoci cike da kayan abinci wajen hana su wucewa abun mamaki ne da ban dariya.

"Ba dukkan kayan abinci ne da suke tarewa ba yana fitowa ne daga Arewa maso yamma ko Arewa maso gabas ba, yawanci daga Arewa ta tsakiya ne. Su kuma ba su ma damu da hakan ba."

KARANTA WANNAN: HarsaHarsashin bindiga ba zai magance ƴan bindiga ba, Adamu Garba

"Hausa-Fulani su ne za su zama shashashu a wannan abu da ke faruwa kuma su ne kasuwancinsu zai tsaya. Ƴan kudanci dai za su iya yin maleji da abin da suke da shi. Don haka, wannan faɗa ne da ba za su yi nasara ba."

"Kamar ma ba su fahimci lamarin ba ne. Su fa Kudanci na ƙorafi ne a kan Fulani makiyaya da ke lalata musu gonaki da kuma ayyuka marasa kyau kamar: garkuwa da mutane da fyaɗe da kuma kashe-kashe.

"A maimakon shuwagabannin Arewa su mai da hankali wajen damƙe su, sai suka ɓuke da yin wani abu daban. Kudancin ƙasar sun yi haƙuri mai yawa, amma lokaci ya yi da za kawo ƙarshen wannan abu."

Arewa ba za ta iya yin nasarar jefa kuduncin ƙasar nan a yunwa ba
Prof. Abiodun ɗan Najeriya mazaunin Afirka ta Kudu Tushe: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

"Sun kasa fahimtar yadda suke tunani. Gwamna guda ne ya fito yana goyon bayan su wajen riƙe bindiga AK 47 domin kiwon shanunsu. Waye ya ba su wannan dama? Kuma irin waɗannan shuwagabanni da wasu Fulani ke cewa, a bar maganar ƙasa, su Najeriya ta su ce. Na gaza fahimtar ko sun san ma me ake nufi da ƙasa?"

KARANTA WANNAN: satar yan matan Zamfara: ‘Yan jarida tsun tsallake rijiya da baya

Akwai Yarabawa masu yawa a Tarayyar Benin da Togo, amma ba za mu iya kiransu da Yaruba ba kuma wannan haka yake a ko'ina a duniya. A Afirka ta kudu, akwai ƙabilu masu yawa da suke warwasu a iyakokin ƙasar. Akwai Tswana da Botswana, amma shi Tswana a Botswana ba zai yi iƙirarin cewa shi ɗan Afirka ta kudu ba ne. Haka abun yake ga mutanen Sotho a dai Afirka ta kudun da Lesotho. Ga kuma Ndebele a Zimbabwe da Afirka ta kudu. Anya kuwa, manene takamaimai ke damun Fulani? Ya tambaya."

A wani labarin, Motoci dari daya dauke da albasa tan 4,000 sun bar Sakkwato zuwa wasu kasashen Afirka sakamakon rikicin kwanan nan day a afku a kasuwar Shasa da ke Ibadan, Jihar Oyo.

Rahotanni sun kawo cewa rikicin Shasa ya yi sanadiyyar mutuwar dillalan albasa 27 yayin da aka kona manyan motoci 14 kurmus.

Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Sannan marubuci kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng