Rundunar Sojoji ta cafke dilolin kwaya tare da miƙa wa NDLEA domin cigaba da bincike

Rundunar Sojoji ta cafke dilolin kwaya tare da miƙa wa NDLEA domin cigaba da bincike

-Rudunar sojin Najeriya sun cafke wasu sai da ƙwayoyi a jihar Cross River.

-Hukumar NDLEA ce ta karɓe su tare kuma da tabbatar cigaba da bincike.

-Mutanen biyu da matasa kuma yanzu haka sun shiga koma.

Rundunar sojin Najeriya da ke jihar Cross River ce ta miƙa wa wasu mutum biyu da ake zargi diloli ga hukumar Hana Sha da Safarar Muyagun ƙawayoyi domin a cigaba da bincike tare da hukunta su.

Mutanen dai su ne Effanga Effanga mai shekaru 37 da kuma Eno-Obong Udeme ɗan shekara 34 waɗanda wasu sojoji da ke ƙarƙashin jihar da ake aiki na musamman 'Operation Akpakwu.'

Babban jami'in da ake kula da runduna ta 13 na 'Brigade Provost Company' mai suna Stanley Ikpeme ne ya miƙa su ga jami'an na hukumar ta NDLEA a madadin Kwamanda, Mohammed Abdullahi, a Calabar.

Rundunar Sojoji ta cafke dilolin kwaya tare da miƙa wa NDLEA domin cigaba da bincike
Rundunar Sojoji ta cafke dilolin kwaya tare da miƙa wa NDLEA domin cigaba da bincike Tushe: Premium Times
Asali: UGC

Stanley Ikpeme yace, "An umarce ni da miƙa wa hukamar NDLEA waɗanda ake zargi da safarar mugayen ƙwayoyi domin cigaba da bincike."

"Waɗannan mutane da ake zargi mun kama su ne a layin Nelson Mandela a Calabar da kuma Ekpenyong Ekpo na ƙaramar hukumar Akpabuyo ta Cross River da ke ɗauke da sinadarai da muke zargin ƙwayoyi ne."

"Saboda haka, an umarce ni da in danƙa su a hannunku, NDLEA, domin cigaba da bincike da hukunta su."

"Sannan muna roƙonku da ku sanar da mu sakamakon bincikenku domin mu ƙara cikin bayananmu," in ji Ikpeme.

Karanta wannan: Sallamar Salihu Tanko Yakasai daga matsayin hadimin Ganduje ya janyo cece-kuce

Abubakar Mohammed, babban ma'aikacin sintiri na NDLEA a Cross River, ya amshi waɗanda ake zargin a madadin hukumar.

Gwamnatin jihar ce dai ta kafa Ofarashin Akpakwu domin magance laifuka a jihar wacce tai nasarar rushen ginunnuka ciki har da otel-otel da ke da alaƙa da wasu laifuka a cikin jihar.

A wani labarin kuma, fastoci dauke da hotunan Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi na neman takarar shugaban kasa a shekarar 2023 sun bazu a jihar Adamawa.

Fastocin da aka fi gani a wasu muhimman wurare a Yola, babban birnin jihar Adamawa na dauke da rubutu da ke tallata Yahaya Bello a matsayin wanda ya dace ya zama shugaban kasar Nigeria.

Anas Dansalma Yakasai ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci ne mai aikin fassara da rahoto a Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Online view pixel