IGP: helikwaftoci na shawagi domin gano inda ɗaliban makarantar Jangebe suke
-A yau ne dai aka sace ɗalibai mata a Zamfara kusan 317 waɗanda izuwa yanzu babu labarinsu.
-Wannan ne ya sa jami'an tsaro tashi tsaye domin ganin sun kuɓutar da su.
-A bisa wannan dalili ne aka tashi helikwaftoci domin yin sintiri wajen lalubo inda suke.
Shugaban rundunar ƴan sanda ta ƙasa, Muhammad Adamu, ya ba da izinin tashin jiragen helikwafta don yin zaryar gano inda ɗaliban makarantar ƴan matan sakadiren Jangebe ta jihar Zamfara.
Wasu masu garkuwa da mutane ɗauke da bindugu a cikin daren Juma'an nan ne suka sace ɗalibabi mata guda 317.
Karanta Wannan: Yanzu-yanzu: Baku fi ƙarfin gwamnati na ba, Buhari ya gargaɗi ƴan bindiga
Tura waɗannan jirage dai ƙari ne kan jami'an tsaron ƙasa waɗanda aka riga aka tura "operation Puff Adder II"
"Jami'ai masu sunturi daga rundunar ƴan sanda sun shiga laluben waɗannan yara na Jangebe da aka sace a ranar Juma'a, 15 ga watan Fabarairu," a faɗar jami'in.
"Wannan ƙari ne dai kan jami'an da aka riga aka tura a waɗanda ke ƙoƙarin maganin ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauran laifuka masu kama da haka."
Shugaban ƴan sandan, a yayin da yake Allah-wadai kan mummunan aikin na sace ƴan matan, ya tabbatar da ƴan sanda da sauran jami'an tsaro ba za su gajiya ba wajen gano yaran da kuma kai su ga iyalansu.
Karanta Wannan: Gwamnan jihar Zamfara ya bada umurnin kulle dukkan makarantun kwana a jihar
Ƴan sandan sun ce wannan samame na haɗin guiwa ne tsakanin ƴan sanda da sojoji da kuma sauran jami'an tsaro da suke samun taimakon gwamnonin jihohin da kuma na sauran masu ruwa da tsaƙi.
IGP dai ya buƙaci al'umma da su kwantar da hankulansu, musamman na jihar Zamfara, sannan ka da su gajiya wajen ba wa ƴan sanda muhimman bayanai waɗanda za su taimaka wajen ceto waɗannan ɗalibai.
A bangare guda, Gwamnatin jihar Zamfara, Muhammad Matawalle, ta bada umurnin rufe dukkan makarantun kwana dake jihar gaba daya.
Matawalle ya yi hakan sakamakon sace daliban makarantar sakandaren GGSS Jangebe da aka sace a karamar hukumar Talata Mafara dake jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Juma'a a Gusau, birnin jihar.
Anas Dansalma ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Sannan marubuci kuma mafassari da ke aiki da Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.
Ku biyo ni @dansalmaanas
Asali: Legit.ng