Magana Ta Fito, An Ji Abin da Tinubu Ya Shirya Yi a Shekaru 2 na Farko bayan Ya Ci Zaben 2027
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya fara bayanin ayyukan da zai yi idan yan Najeriya sun sake zaben shi a karo na biyu a 2027
- Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da tsare-tsaren tattalin arziki da za su amfani jama'a
- Ya bayyana cewa ya san mutane sun rika sukarsa lokacin da ya fara daukar matakai masu tsauri bayan rantsar da shi a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa zai ƙara ƙaimi wajen magance matsalolin ƙasa tare da ci gaba da sauye-sauyen da gwamnatinsa ta fara idan aka sake zaɓensa wa’adi na biyu.
Tinubu ya furta hakan ne a jawabinsa a taron shekara-shekara na Africa CEO Forum da aka gudanar a Kigali, ƙasar Rwanda, inda ya yi waiwaye kan manufofin tattalin arziki da salon mulkin gwamnatinsa.

Kara karanta wannan
'Ka yi hattara,' Malami ya hango wasu gwamnonin Arewa za su yaudari Tinubu a 2027

Source: Twitter
Tribune Nigeria ta ruwoato cewa da yake amsa tambaya kan abin da ‘yan Najeriya za su iya tsammani a shekaru biyun farko na wa’adi na biyu, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta kara kaimi.
Shugaba Tinubu zai kara kaimi
Shugaban kasa ya tabbatar da cewa zai ci gaba da aiki tukuru saboda yanayin duniya na buƙatar sauye-sauye da sababbin dabarun shugabanci a koda yaushe.
Ya bayyana cewa salon shugabancinsa ya ta’allaka ne kan ɗaukar matakai masu ƙarfi da gaggawa domin amfanin jama’a, yana mai cewa jinkiri wajen yanke hukunci kan jawo gazawa.
A cewarsa, sauye-sauyen da aka fara aiwatarwa sun fara haifar da sakamako mai kyau, inda tattalin arzikin ƙasar ya fara samun daidaito tare da samar da damar tsara kasafin kuɗi cikin sauƙi.
Shugaban ya kuma ce darajar Naira ta fara samun daidaito, yayin da gwamnati ke tallafa wa marasa ƙarfi ta hanyar rabon tallafin kuɗaɗe kai tsaye da shirye-shiryen tallafin ilim, cewaf rahoton The Nation.
Abin da Tinubu zai yi a wa'adi na 2
Da yake amsa tambaya kan abin da zai yi a shekaru biyun farko idan aka sake zaɓensa, shugaban ya ce:
“Za a ga ƙarin aiki, akwai ƙarin ƙalubale masu tarin yawa, duniya ba za ta jira kowa ba. Dole ne gwamnati ta ci gaba da sake tunani da kawo sababbin dabaru.
“Salon da na zo da shi a shugabanci shi ne ce imani da cewa shugaba mai kawo sauyi shi ne wanda yake iya ɗaukar mataki a lokacin da ya dace domin jama’a. Idan ka rasa wannan dama, to ba ka kan hanyar nasara.
“Shi ya sa tun farko na ɗauki matakai masu wahala duk da raɗaɗin da suka haifar. Na daina karanta jaridu da sharhi saboda na san zan fuskanci suka mai yawa, kuma hakan ya faru.

Source: Facebook
Tinubu ya koka kan tsadar kudin ruwa
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce kusan rabin kudaden shiga na Najeriya a 2026 za su tafi ne wajen biyan basussuka.
Ya ce duk wata Dala da kasar ke kashewa wajen biyan kudin ruwa mai tsada na rage damar zuba jari a muhimman bangarorin tattalin arziki.
Ya ce tsarin hada-hadarr kudin duniya na yanzu na kawo cikas ga kokarin Afirka na bunkasa masana’antu saboda wahalar samun rance mai saukin ruwa.
Asali: Legit.ng

