Boris Johnson ya taya Ngozi Iweala murnar zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya

Boris Johnson ya taya Ngozi Iweala murnar zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya

-Kwanan bayan nan ne dai tsohuwar ministan kuɗin Najeriya ta kafa tarihi.

-Ngozi ta zama mace ta farko da ta fara zama shugabar kasuwanci na duniya, inda za ta shiga ofishinta a 1 ga watan Maris, 2021.

-ƙasashe da yawa dai sun taya ta murna, inda Boris Jonson ya nasa a shafinsa na Tuwita.

Boris Jahnson @BorisJohnson, firaministan ƙasar Ingila ya taya Ngozi, tsohuwar ministan kuɗi ta Najeriya a lokacin mulkin Janathan kuma sabuwar shugaban ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya murna a kafar sada zumunta ta Tuwita.

KU DUBA: An gano dajin da yan bindiga suka ajiye yan matan makarantar Jangebe

Saƙon na Jahnson na nuni da wata gaisawa cewa sun gaisa da Ngozi a inda yake cewa; "Madalla da gaisawa da ke @NOIweala kuma ina taya ki murnar kan wannan shugabanci.

Firaministan Ingila ya taya Ngozi Iweala murnar zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya a Tuwita
Ngozi kenan, mace ta farko da ta zama babbar darkatan WTO Tushe: @NOIweala
Asali: UGC

"Wannan ta Ƙungiya Kasuwancin Duniya na da muhimmiyar rawa da za ta taka wajen tabbatar tsarin ba-cuta-ba-cutarwa a yayin da duniya ke farfaɗowa daga annobar Kwabid-19," in ji Johnson.

Ngozi ta amsa da yi masa da godiya tare da yaba masa kan tattaunawar da suka yi mai amfani kan yadda za a inganta ƙungiyar da kuma jagorancin ƙungiyar da ya yi a lokacin taron ƙasashe bakwai masu cikakkken iko (G7).

DUBA NAN: Ranar NGOs ta duniya: Minista Sadiya ta yabawa kungiyoyin tallafi kan ƙoƙarin da suke yi

"ƴunkuri na inganta Ƙungiyar Kasuwancin Duniya, da shigowa da farfaɗo da ita daga lahanin annobar Kwabid-19 abu ne mai muhimmanci. Wannan ƙungiya a shirye take ta yi aiki da kai," a cewar Ngozi.

Daga jihar Barno kuwa, wata mota ɗauke da ma’aikatan wutar lantarki da dama da kuma wani jami’in tsaro sun ci karo da wani abin fashewa a safiyar Asabar din nan a jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya, HumAngle ta ruwaito rahoto.

Wadanda lamarin ya rutsa da su na daga cikin tawagar da ke aikin dawo da wutar lantarki a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, bayan da kungiyar ISWAP ta lalata wata hasumiyar wuta a sanannen yankin Mainok da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Sun lalata hasumiyoyin wutan lantarki da dama yayin da Kamfanin Yada Wutan lantarki na Najeriya (TRCN). ke gyara wanda ya lalace mai karfin 330kV.

Anas Dansalma Yakasai ya nazarci harshen Hausa a Jami'ar Bayero, Kano. Marubuci ne mai aikin fassara da rahoto a Legit Hausa. Burinsa zama babban ɗan jarida domin samar da sahihan labarai.

Ku biyo ni @dansalmaanas

Asali: Legit.ng

Online view pixel