Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi wa 'Yan Arewa Barazana kan Zaben 2027? Gaskiya Ta Fito

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi wa 'Yan Arewa Barazana kan Zaben 2027? Gaskiya Ta Fito

  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio bai yi kalaman rashin da'a ko barazana da 'yan Arewa gabanin zaben 2027 ba
  • Ofishin shugaban majalisar ya yi fatali da wani faifan bidiyo da ake yadawa a kafafen sada zumunta, ya ce karya ce tsagwaronta
  • Ya buƙaci ‘yan Najeriya, musamman mutanen Arewa, su yi watsi da zargin tare da gujewa duk wani abu da zai wargaza hadin kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya musanta rade-radin da ake yadawa cewa ya yi wa yan Arewa barazana kan zaben 2027.

Sanata Akpabio ya yi watsi da faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ake zargin ta yi kalaman da ka iya haddasa rarrabuwar kai gabanin zaɓen badi.

Akpabio.
Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio yana jagorantar zaman sanatoci a Abuja Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Leadership ya ce hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Majalisar shawara kan harkokin ‘yan Najeriya mazauna waje da ƙungiyoyi masu zaman kansu, Jibril Tafida, ya fitar ranar Juma’a a Abuja.

Kara karanta wannan

Magana ta fito, an ji abin da Tinubu ya shirya yi a shekaru 2 na farko bayan ya ci zaben 2027

Da gaske Godswill Akpabio ya yi barazana?

Ofishin shugaban Majalisar dattawan ya bayyana zargin a matsayin ƙarya, mugunta da kuma wani yunƙuri na haddasa tashin hankali a ƙasa.

Bidiyon da ke yawo ya yi zargin Akpabio ya ce dole ne ‘yan Arewa su zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 ko kuma su fuskanci kora daga Najeriya, zargin da ofishinsa ya ce ba gaskiya ba ne.

“Muna so mu bayyana a fili cewa Shugaban Majalisar Dattawa bai taɓa yin irin wannan magana ba.
"Wannan zargi ƙarya ce tsagwaronta, cike da mugunta kuma wani yunƙuri ne na yaudarar jama’a da haddasa tashin hankali,” in ji sanarwar.

A nemi jami'an tsaro su gudanar da bincike

Ofishin Akpabio ya kuma buƙaci hukumomin tsaro su binciki tare da kama Garus Gololo, mutumin da ya bayyana a bidiyon, domin ya tabbatar da inda da lokacin da Akpabio ya yi irin wannan magana.

Sanarwar ta kuma yi tir da abin da ta kira amfani da “kalamai mara dadi,” kan Akpabio, tana mai cewa irin hakan na rage mutuncin manyan muƙaman gwamnati da kuma cibiyoyin dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Hayatudeen: "Matakin da zan dauka kan 'yan bindiga idan na zama shugaban kasa"

Sanatoci.
Yan Majalisar dattawan Najeriya yayin da suke tsakiyar zama a Abuja Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Ofishin Akpabio ya caccaki Gololo

Ofishin ya zargi Gololo da yawan yin kalamai na cin mutuncin Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, yana mai cewa hakan na da alaƙa da siyasa, cewar rahoton Daily Post.

“Garus Gololo ya saba zagin Shugaba Bola Tinubu da APC domin faranta ran masu ɗaukar nauyinsa a siyasa. Dole ne a kawo ƙarshen hakan,” in ji sanarwar.

Daga ƙarshe, ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ya buƙaci ‘yan Najeriya, musamman mutanen Arewa, su yi watsi da zargin tare da gujewa duk wani abu da zai iya haddasa rarrabuwar kai ko yaɗa bayanan ƙarya a ƙasar.

Tinubu ya gana da tawagar sanatoci

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya gana da Shugabannin majalisar dattawa a fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya na Abuja.

An bayyana ganawar a matsayin mai muhimmanci kuma ta gaggawa, inda aka ce ta biyo bayan wasu shawarwari da aka yanke a zaman sirri na majalisar.

Wasu sanatocin sun nemi a ba su tikitin takara mai tsaye wanda aka ce shugaban bai amince ba kuma ya nace cewa dole a mutunta tsarin jam’iyya

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262